Yadda rikici tsakanin Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ya sa farashin fetur ya tashi

Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman tare da takwaransa na Abu Dhabi Mohammed bin Zayed, a Abu Dhabi, 27 Nuwamba 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sannu a hankali rashin jituwar ke bayyana a kawancen da Saudiyya da Yarima mai jiran gadon sarautar Abu Dhabi suka kulla
    • Marubuci, Daga Sameer Hashmi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East business correspondent

Takaddamar da ta kaure a bainar jama'a a wannan makon tsakanin Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa kan yawan man fetur din da kowaccensu za ta fitar, ta sa sun yi watsi da tattaunawar da suke yi, lamarin da ya janyo farashin fetur ya yi tashin da bai taba yi ba cikin shekaru shida.

Dole ta sanya kasashe 23 da ke cikin kawancen OPEC, wanda ya hada da kungiyar kasashen da ke fitar da man fetur da kasashen da ke samar da shi kamar Rasha, ɗage da tattaunawar da suke yi sai yadda hali ya yi. Wannan ya jefa tsoro kan makomar kungiyar da ta shafe watanni 18 cikin halin rashin tabbas sakamakon barkewar annobar korona da ta sanya tattalin arzikin duniya ya shiga mummunan yanayi.

A makon jiya ne matsalar ta fara, bayan Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi watsi da tayin Opec da shugabannin kasashen Saudiyya da Rasha ta kara wa'adin watanni takwas domin rage man da take fitarwa.

Tambarin kungiyar Opec

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kawo yanzu Opec da sauran kasashen ba su sanya lokacin da za su yi zaman tattaunawa ba

Burin Hadaddiyar Daular Larabawa shi ne sake sasantawa kan yarjejeniyar da ake kai a yanzu, wadda ake duba abin da aka samar da ragewa ko kara lissafin ta yadda za ta samu 'yancin kara yawan man da ta ke fitarwa. Sai dai Saudiyya da Rasha kuma ba sa goyon bayan hakan.

Sasantawar ta dauki salon da ba a saba da shi ba a lokacin da ministocin makamashi na Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, wadanda aminan juna ne, suka fara bayyana mabambanta ra'ayi kan batun, lamarin da ya sa aka gane akwai baraka tsakanin kasashensu.

"Kowa ya yi mamakin takaddamar, sai dai ta yiwu lamari ne da ba za a iya kaucewa faruwarsa ba," in ji Ben Cahill, babban jami'i a Cibiyar Tsare-Tsare da Nazari kan Harkokin Kasashen Waje da ke Washington.

Ya kara da cewa "Yawan man da Abu Dhabi ke samarwa ya fi wanda yarjejeniyar Opec ta amince kasar ta fitar. Ta kashe makudan kudade domin kara yawan man da take samarwa. A yanzu kuma bukatar man na karuwa, wannan ya sa Hadaddiyar Daular Laraba ke tsaka mai wuya tun shekarar da ta gabata, saboda gaza kara man da take hakowa."

Yarimomi

Shekaru da dama, dangantaka tsakanin kasashen biyu makwabtan juna ta yi tasirin daidaita siyasar yankin Gabas Ta Tsakiya. Kyakkyawar alakar da ke tsakanin Yarima mai jiran gadon masarautar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed, da takwaransa na Saudiyya ta kara yaukaka kawancen kasashen biyu.

Mayakan da ke goyon bayan gwamnatin Yemen dauke da bindiga samfurin mashinga, a lokacin fafatawa da mayakan kabilar Houthi a yankin Marib da ke Yemen ,16 Maris 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Saudiyya da Daular Larabawa na goyon bayan bangaren gwamnati a yakin basasar da aka kwashe shekaru shida ana yi a kasar Yemen

Ana yi wa mutanen biyu kallon wadanda ke jan ragamar kasashensu da karfin iko.

An kwashe shekaru da dama ana hadin kai tsakanin kasashen kan batutuwa masu muhimmancin gaske. Sun kafa hadakar rundunar sojin kasashen Larabawa a 2015 domin yaki da yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran a Yemen, sannan suka sanya takunkumin difilomasiyya da cinikayya da tafiye-tafiya kan Qatar a 2017.

Sai dai shekaru biyu da suka wuce baraka ta fara bulla tsakaninsu, lokacin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta janye wasu daga cikin dakarunta daga Yemen, lamarin da bai yi wa Saudiyya dadi ba.

A watan Janairu ne Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince da kawancen da Saudiyya ke jagoranta, wajen cire takunkumin da suka sanya wa kasar Qatar, duk da cewa suna nuna shakku kan manufar hakan.

Haka kuma Saudiyya ta nuna rashin gamsuwa kan matakin Hadaddiyar Daular Larabawa na sasantawa da kasar Isra'ila a shekarar da ta gabata.

'Yan jarida sun shaida zuwan wakilan Qatar gabannin taron kolin kungiyar kasashen larabawa na 41, da Saudiyya ta karbi bakunci a birnin al-Ula (5 Junairu 2021)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A watan Junairu kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar suka amince su yi tafiya daya a taron koli da suka yi

Har wa yau, a watan Janairu ne dangantaka tsakanin kasashen ta kara munana, lokacin da Saudiyya ta bai wa kamfanonin mai wa'adin mayar da hedikwatocinsu zuwa kasar kafin shekarar 2024, ko su rasa kwangilolin gwamnati. An kalli hakan a matsayin martani ga Hadaddiyar Daular Larabawa wadda ita ce ja-gaba a wannan fannin a yankinsu.

Bayan Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi watsi da yarjejeniyar Opec, Saudiyya ta mayar da martani ta hanyar hana jiragen Daular shiga kasar tare da fakewa da barkewar sabon nau'in cutar korona.

Sai dai lamarin ya zo a daidai lokacin da ake hutun karamar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan, lokacin da mutane da dama ke shirin tafiya hutu Hadaddiyar Daular Larabawa.

Gasar bunkasa tattalin arziki

Kokarin da Opec ke yi na samun matsaya kan haka da fitar da man fetur, ya kara janyo gasar bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ke kokarin karkatar da akalar samun kudade daga kan fetur da bisa al'ada aka dogara da shi.

Yayin da Saudiyya ke daukar tsauraran matakan bunkasa tattalin arziki karkashin jagorancin Yarima Mohammed bin Salman, sun fara gasa ta Hadaddiyar Daular Larabawa a fannonin yawon bude ido, da fasahar zamani.

"Saudiyya ita ce ja-gaba a yankin, wadda a yanzu ta farka daga baccin da take yi domin bunkasa tattalin arzikinta. Ta wani fannin kuma, ta damu matuka kan Hadaddiyar Daular Larabawa," in ji Neil Quilliam, na Chatham House a birnin Landan.

Hoton rukunin gidajen skyline a Dubai (12 Juni 2021)

Asalin hoton, Reuters

"Nan da shekaru 15 zuwa 20, idan tsarin Saudiyya na bunkasar tattalin arziki ya kai gaci, to hakan zai zama babbar barazana ga tattalin arzikin Hadaddiyar Daular Larabawa

Kawo yanzu babu tabbacin ko kasashen biyu za su amince da sabuwar yarjejeniyar Opec.

Sai dai Ali Shihabi, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mai kusanci da masarautar Saudiyya, bai amince takaddamar za ta yi tasirin raba su ba, duk da cewa matakin na Hadaddiyar Daular Larabawa ya zo da ban mamaki ga Saudiyya, musamman ganin yadda aka sha wuya kafin cimma matsaya.

"Dukkan bangarorin biyu, sun dade ba su da ra'ayi guda kan manyan batutuwa. Kuma daman ana samun matsoli nan da can tsakanin kasashe, misali hakan ta faru tsakanin Amurka da Birtaniya. Sai dai hakan ba zai iya shafar ginshikin kawancensu ba."