Bethel Baptist High School: 'Yan bindiga sun sace 'dalibai 150' a jihar Kaduna

Kwamishinan Tsaro na Kaduna Samuel Aruwan

Asalin hoton, Kaduna State Govenment

Bayanan hoto, Gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba zuwa yanzu

Bayanai sun tabbatar da sace dalibai da dama a wata makarantar sakandare da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeirya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a sakandaren Bethel Baptist High School, Damishi da ke Karamar Hukumar Chikun da asubahin Litinin tare da sace dalibai da dama.

Kamfanin dillancin labaria na Reuters ya ambato mahaifin wani dalibi yana cewa kusan 150 ne ba a gani ba bayan harin da 'yan bindigar suka kai.

Sai dai hukumomi sun ce sun ceto mutum 26 daga cikin wadanda aka sace.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, wanda ya tabbatar wa BBC Hausa labarin, ya ce dansa yana cikin daliban makarantar amma ya kubuta.

Duk da yake ba a san adadin daliban da aka sace ba, Rabaran Hayab ya ce a ranar Juma'a mun kirga "dabilai 180 da suke ɓangaren kwana amma a safiyar nan yaran da muka samu ba su fi 24 zuwa 27 ba".

"Muna sa ran dai waɗannan ɓuya suka yi a wani wuri amma dai waɗancen an tafi da su," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "Da ma ranar Juma'a an yi ganawa da malamai tun da abubuwa [na rashin tsaro] suna faruwa ko za a cire yaran daga makaranta.

Sai dai Rabaran Hayab ya ce jami'an tsaro sun yi wa makarantar kawanya.

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya fitar ta ce "jami'anmu sun fafari 'yan bindigar ta hanyar amfani da dabaru da makamai kuma sun yi nasarar ceto dalibai 26 ciki har da wata malama guda daya cikin koshin lafiya.

Ana ci gaba da neman dukkan daliban domin tabbatar da cewa an ceto su cikin koshin lafiya," a cewarsa

'Yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe mutum bakwai a ƙarshen mako a Jihar Kaduna.

A ranar Asabar Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya cire ɗansa daga makarantar gwamnati saboda 'yan fashi na ynƙurin sace shi.

Maza da mata

Makarantar ta Bethel Baptist High School ta ƙunshi maza da mata sannan kuma akiwa waɗanda ke kwana da kuma masu zuwa kullum.

"Ɗana da aka ɗauka namiji ne amma wanda ya faɗa mani labarin ya ce 'yarsa aka ɗauka, sai dai sun kuɓuta tare," a cewar Mista Joseph Hayab.

Ya ƙara da cewa yaran da suka kuɓuta suna hannun hukumar makaranta ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.