Nasir El-Rufai: Na cire ɗana daga makarantar gwamnati saboda 'yan fashi na ƙoƙarin sace shi

Asalin hoton, KDSG
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa ya cire ɗansa a asirce daga makarantar gwamnati da ya saka shi.
Jaridar Daily Trust ce ta fara ruwaito yadda gwamnan ya cire Abubakar Sadiq El-Rufai mai shekara shida daga makarantar Kaduna Capital wadda ya saka shi a 2019.
Cikin wata hira da BBC Pidgin, El-Rufai ya ce ya cire shi ne saboda yadda 'yan fashin daji ke ƙoƙarin kai wa makarantar hari domin sace yaron nasa, musamman saboda a kare rayuwar sauran yara.
Ya ƙara da cewa ya saka 'yarsa ma mai suna Nesrin a makarantar lokacin da ta cika shekara shida da haihuwa.
"Mun cire su ne na ɗan wani lokaci saboda tsaron makarantar, saboda mun daƙile harin 'yan fashi har sau biyu a kan makarantar da ke yunƙurin sace ɗana.
"Ba na tunanin za su samu nasara saboda akwai cikakkun jami'an tsaro a wurin amma za a saka rayuwar sauran yaran cikin haɗari...suna so su ga idan suka sace ɗan nawa zan biya kuɗin fansa ko ba zan biya ba."
Gwamnan ya ce yanzu haka yaran suna gida, inda ake yi musu darasi amma za su rubuta jarrabawa a makarantar.
Cika alƙawarin kamfe

Asalin hoton, KDSG
Tun a 2017 Gwamna El-Rufai ya yi alƙawarin saka ɗansa a makarantar gwamnati domin nuna jajircewarsa wajen gyara harkar ilimi a Kaduna.
A ranar 21 ga watan Satumban 2019 ne gwamnan da mahaifiyar Abubakar, Ummi El-Rufai, suka yi wa ɗan nasu rajista a makarantar Kaduna Capital tare da rakiyar wasu jami'an gwamnati.
Duk da cewa gwamnan ya cika alƙwarin, wasu na cewa ya yi hakan ne kawai don ya cimma manufa ta siyasa. Sai dai El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta ɗauki ilimi a matsayin abu na farko da za ta gyara.
"Ni ɗan talakawa ne amma 'ya'yana za su bigi ƙirji su ce su 'ya'yan wasu ne saboda ilimi. Mahaifina ya rasu ina ɗan shekara takwas kuma makarantar gwamnati na yi har na kawo wannan matsayin.
"Na tattauna da tawagata mun yanke shawarar cewa mu mayar da ilimi ya zama muradinmu na farko ta yadda kowane yaro a jihar nan zai samu ilimin."











