Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka sace mutum 22 har da jarirai a Kaduna
'Yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun sace tare da kashe mutum aƙalla 29 a Jihar Kaduna a ranakun ƙarshen mako.
Bayanai sun ce wasu mahara ɗauke da manyan makamai sun shiga garin Zariya da tsakar dare zuwa wayewar garin Lahadi, inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi sannan suka kutsa cikin wani asibitin masu larurar kuturta a garin.
Wani ma'aikacin asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa 'ƴan bindigar sun sace aƙalla mutum 12, ciki har da yara 'yan ƙasa da shekara uku guda uku da kuma matashiya da ba ta kai shekara 20 ba.
Sai dai ya ce daga baya mutum biyu sun kuɓuta daga hannun maharan.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan ya ce "ba mu tantance adadin waɗanda aka sace ba saboda ba mu kammala bincike ba".
"An sanar da jami'an tsaro amma kafin su zo 'yan bindigar sun tafi," in ji mutumin.
An kashe mutum bakwai
A wasu hare-haren daban kuma, 'yan bindigar sun kashe aƙalla mutum bakwai a yankunan Jihar Kaduna cikin kwana uku.
Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya ce jami'an tsaro ne suka shaida wa gwamnati faruwar lamarin, kodayake bai tantance ranakun da kowane lamari ya faru ba.
Wani rahoton kafar Channels TV ya ce maharan sun yi awon gaba da mutum aƙalla 10 a Iri Station da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru.
Maharan sun afka wa garin ne da misalin 1:00 na dare, a cewar wani mazaunin yankin mai suna Moses Matthew.
A cewar Mista Aruwan, 'yan fashi sun harbe mutum huɗu a wajen garin Tsohon Gayan da ke Ƙaramar Hukumar Chikun.
Kazalika, an kashe wasu mutum biyu da aka bayyana da suna Solomon Bamaiyi da Francis Moses a Kakau, sannan aka kashe wani da ba a bayyana sunansa ba a Kachia.
Ya ƙara da cewa wani mai suna Danjuma Alhaji mazaunin Tsohon Farakwai na Ƙaramar Hukumar Igabi ya rasa ransa a hannun 'yan fashin a garin Galadima na Ƙaramar Hukumar Giwa.
Kwamishinan wanda ya jagoranci tawagar jami'an tsaro zuwa wuraren da aka kai hare-haren, ya bayyana su da "rashin tausayi" sannan ya ce jami'an tsaro na bakin ƙoƙarinsu wajen kawo ƙarshen matsalar.