Gabon ta zama kasar Afirka ta farko da ake biya kudi domin ta kare gandun dajinta

Asalin hoton, Getty Images
Gabon ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta karɓi kuɗi don rage hayaƙi mai gurɓata yanayi ta hanyar kare dajinta.
Shirin Kare dazuka na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira (Cafi) ya mika Dala miliyan 17, a matsayin kaso na farko na yarjejeniyar dala miliyan 150 da aka cimma a shekarar 2019.
Kusan kashi 9 cikin 100 na Gabon na da gandun daji, kuma suna da muhimmanci wajen zuƙe hayaki mai gurbata muhalli a duniya.
Gabon ta iya nuna cewa ta yi nasarar rage sare dazuka, don haka ta rage hayakin da take fitarwa a shekarar 2016 da 2017 idan aka kwatanta da shekarun da suka gabata, kamar yadda shirin na Cafi ya bayyana.
Sakamakon haka, Norway ta biya Gabon Dala miliyan 17 don rage yawancin iskar carbon da ba don kokarin na Garbon ba da yanzu watakila an sake ta ta gurbata yanayin duniya.
Biyan farko yana wakiltar kashi 0.1 na kudaden shigar da Gabon ke tarawa a kowacce shekara, amma Ministan gandun daji na kasar Lee White ya shaida wa BBC cewa wannan wani muhimmin mataki ne na farko.
Ministan ya ce Norway ta tabbatar da tsarin Gabon na sanya ido kan sare dazuzzuka da kawar da hayakin carbon, wanda hakan zai taimaka wa kasashen da ke fitar da hayakin wajen biyan Gabon don sarrafa albarkatunta a gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Gabon ta ƙaddamar da wasu tsare-tsare na kiyayewa a cikin 'yan shekarun nan, ciki har da ƙirƙirar wuraren shakatawa na ƙasa 13 da kuma aikin yaƙi da sare bishiyoyi ba bisa ƙa'ida ba.
Duk da haka, kasar na son samun karin kudi daga harkar katako kuma ta ce za ta ci gaba da girbin bishiyoyi da kara darajar bangaren ta hanyar sarrafa karin danyen kaya a gida.
Kungiyar bayar da agaji ta Burtaniya mai suna Charity Rainforest Foundation wacce ke aikin yaki da sare dazuka ta shaida wa BBC cewa yayin da bada tallafin kuɗi don kare gandun daji ke da muhimmanci, amma wannan biyan "yana da haɗari, duba da cewa zai iya sa wasu kasashen su kwadaita da samun kudin suma''.
Yana nuni zuwa ga bayanai daga kungiyar sa ido ta Global Forest Watch da suka nuna cewa shekarar 2017 ta kasance daya daga cikin mafi girman asara a kasar ta Gabon tun shekarar 2001.
Gwamnatin ta ce bin diddigin da take yi ya nuna cewa kasar za ta iya kula da hakar carbon ta hanyar tabbatar da ɗorewar dazuka.

Sharhin Matt McGrath, wakilin BBC kan muhalli.
Tun tsawon shekaru da yawa, kasashe masu arziki suna neman kawo karshen sare dazuka a Afirka da sauran wurare ta hanyar biyan kasashe matalauta don kare bishiyoyinsu.
Wannan hanyar ta dakatar da guguwar sare bishiyoyi don haka waɗannan sabon sakamakon da ake gani daga Gabon tabbas abun ƙarfafa guiwa ne.
Manyan bishiyoyin da suka jima a Gabon suna da mahimmanci ga duniya yayin da suke zuke iskar carbon fiye da na manyan dazuzzuka ciki har da Amazon, su ma suna da kusan kashi 60 cikin 100 na giwayen da ke rayuwa a Afirka.
Ministan gandun daji na Gabon yanzu yana son ya bullo da wata sabuwar manufa da za ta sa kasashen duniya masu karfi su rika biyan kasarsa kudade don rage fitar da hayaki daga sassa masu wuyar lura, ciki har da na sufuri.
Dayawa suna ganin wannan a matsayin ra'ayi mai ciki da ce-ce-ku-ce, inda zai bar talakawa a cikin wahala.
Tabbas wannan tambayar za ta bayyana a tattaunawa a taron sauyin yanayi na COP26 a Glasgow a watan Nuwamba.












