Ƙayatattun hotunan Afirka na mako: 11-17 Yuni 2021

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga sassan Afirka ko na wasu ƴan nahiyar a sauran sassan duniya a wannan makon, daga ranar 11 zuwa 17 ga watan Yunin 2021.

Two women walking past a mural

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mata biyu na tafiya ta kusa da wani gini da aka yi masa fenti da zane-zane a unguwar Abobo a birnin Abidjan na Ivory Coast a ranar Juma'a.
Two female swimmers with hands raised

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar kuwa was ƴan Masar Hanna Hiekal da Laila Mohsen ne suka kammala gasar ninƙaya a birnin Barcelona na Spain.
Nigeria forward Rasheedat Ajibade tries to kick a loose ball before Portugal goalkeeper Inês Pereira makes the save

Asalin hoton, USA Today Sports

Bayanan hoto, Washegarin ranar kuma ƴar wasan gaba a tawagar ƙwallon Najeriya ta mata Rasheedat Ajibade ta naushi mai tsaron ragar Portugal Ines Pereira a yayin wasan ƙawance na ƙasa da ƙasa da aka tashi 3-3.
A dancer of the Reda Folkloric Troupe with her hands spread

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata ƴar wasan raye-raye kenan take cashewa a wajen wani taro a birnin Alƙahira na Masar a ranar Laraba.
Three women dressed in traditional dresses of the Harari culture of eastern Ethiopia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Lahadi kuwa waɗannan matan da suka yi shiga iri ɗaya a kayan al'adarsu ta Hariri ta gabashin Habasha, sun fita zuwa wani babban taro da aka yi a Dandalin Meskel.
A man holds up a clenched fist during a demonstration in Tunisia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar, masu zanga-zanga sun mamaye wasu sassan babban birnin Tunusiya don nuna adawa da cin zarafin da ƴan sanda ke yi, bayan da wani bidiyo da ke nuna wani ɗan sanda na zane wani yaro ya yaɗu a intanet.
A man harvesting grapes

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Litinin kuwa a Masar, wani ma'aikaci ya ciro inibi a wata gona da ke Khatatba al-Minufiyah, inda yawanci ake fitar da shi ƙasashen Turai.
A woman's hands holding a diamond

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wani lu'u-lu'u da aka bayyana a matsayin na uku mafi girma kenan da aka gano a ƙarƙashin ƙasa a Botswana...
A diamond on a table

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gano lu'u-lu'un mai darajar karat 1,098 ne a ranar 1 ga watan Yuni aka kuma nuna wa Shugaba Mokgweetsi Masisi a babban birnin ƙasar Gaborone.
1px transparent line
A man counting seedlings

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a wani mai aikin sa kai yana ƙirga irin shuka a birnin Accra na Ghana.
A man in an Ivorian flag making a V for victory sign

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Za mu rufe da inda muka fara wato Ivory Coast, inda a nan wani magoyin bayan tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo ne, ke sanye da tutar ƙasar, yana nuna alamun nasara a ranar Alhamis a yayin wani maci gabanin komawar Mr Gbagbo ƙasar.
1px transparent line

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.