Pan-African Parliament: Naushi da barazanar kisa na neman raba kan Afirka

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Dickens Olewe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
An samar da majalisar kishin Afirka da burin hada kan nahiyar, to amma a baya-bayannan Pan-African Parliament (PAP ) ta fada cikin rikicin da har ya sa wasu mambobinta na barazanar kashe juna.
Rikicin na faruwa ne bayan rabuwar kai da ake ta samu kan yankin da zai fito da sabon shugaban majalisar.
PAP na da mambobi 235, kuma 'yan majalisar daga kudancin Afrika sun kafe cewa su ne za su karbi shugabanci kasancewar an dade 'yan sauran yankunan na jagoranci.
''Zan kashe ka'', a cewar dan majalisa daga Afrika ta Kudu Julius Malema, yayin da yake nuna yatsa ga wani dan majalisar.
Daga baya Mr Malema ya yi kokarin kare kansa da kan kalaman, inda ya ce shi ma an yi masa barazana ne.
A wani zaman na daban, wasu 'yan majalisar sim dinga ɗaga murya suna fadin: ''ba batun karba-karba. Ba batun zabe.''
Kuma a daidai lokacin ne wasu su suka dinga kokawa da akwatunan zabe.
Bayan da musayar yawu ta tsananta ne sai kawai aka fara kai naushi, za ma a iya jiyo muryar wani yana cewa ''ku yi maza ku kira 'yan sanda da gaggawa.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a YouTube

Cikin wata hira da BBC, 'yar majalisa daga Zimbabwe, Barbara Rwodzi, ta ce an jikkata ta a hannu yayin daya daga cikin rigingimun da aka yi.
Masu suka sun bayyana lamarin a matsayin abin kunya da Allah-wadai.
A cewar Farfesa Lesibu Teefu na Jami'ar Afirka ta Kudu, ''majalisar ta kara kawo rabuwa ne a nahiyar maimakon hadin kai.''
''Shekaru 60 kenan da samun damar hada kai amma har yanzu ba mu ko kusa da cimma haka ba.''
Kafa majalisar shekaru 17 da suka wuce ya zo ne a wani yunkurin shugabannin kasashen Afrika na wancan lokacin da suka hada marigayi Muammar Gaddafi na Libya, na ganin cewa kasashen Arika sun rika magana da murya daya.
Sun aminta cewa kungiyar Tarayyar Afrika za ta jagoranci tafiyar da nahiyar, to amma tana bukatar majalisa da za ta taimaka ta.

Asalin hoton, Getty Images
To amma masu suka sun ce tun ma kafin a fara rikici da ya hada da baiwa hamata, ba bu wani abu da majalisar ke tsinanawa ban da surutu marar tasiri.
Dan majalisa Toussaint Manga daga Senegal ya fada wa BBC cewa mafi yawan matsalolin sun samo asali ne da rashin saka hannu kan yarjejeniyar Malabo da aka kulla a shekarar 2014, wadda kasashe 11 daga cikin 54 suka ki saka mata hannu.
Kuma dama ana bukatar kasashe 28 su saka hannu kan yarjejeniyar.
A cewarsa: ''Matsawar muna son ciyar da majalisar nan gaba to dole ne mu ba ta hadin kan da take bukata''.

To amma yanzu hankali ya koma kan wanene zai zama sabon shugaban majalisar wanda shine dalilin sabuwar tarzomar da ake samu.
A watan Oktoba ne za a dawo zama, bayan zaman da aka yi a watan da ya wuce an tashi baram baram.
A cewar dan majalisa McHenry Venaani daga Namibia ''yan kasashen gabashi da kuma tsakiyar Afrika ne suka mamaye majalisar da karfi da yaji.''
Yan yankin Kudancin Afrika na so a ba da mulkin ne ga Chif Fortune Charumbia dan kasar Zimbabwe, wanda shine shugaban majalisar na riko a halin yanzu.
Kuma sun shirya hakanne da nufin yin karba-karba a tsakaninsu.

Asalin hoton, Getty Images
To amma ganin cewa da wahala dan takararsu ya kai, sun kafa hujjar adawa da abokin takara daga Mali ko Sudan ta Kudu, kan cewa yankunan na fama da rikici.
A cewar masu adawar yanzu haka juyin mulki biyu a ka yi a Mali kuma kungiyar Tarayyar Afrika ta dakatar da ita.
A Sudan ta Kudu kuwa sun ce yanzu haka ma babu majalisa da ke zama, a don haka su ke zargin sahihancin yan majalisa daga yankin.
To amma a gefe daya masu suka basu gamsu da bayar da mulki a Zimbabwe ba inda har yanzu jam'iyyar Zanu-PF ke mulki tun shekarar 1980.
Sai dai masana harkokin siyasa a Afrika ta Kudu sun ce sun ji kamshin sauyi mai ma'ana a majalisar PAP, kuma matasan yan siyasa ne za su kawo shi.
A cewar Sophie Mokoena ''muna bukatar majalisa ta tabbatar yarjejeniyar Malabo ta tsallake kuma an bincike tsohon shugaban PAP da ake zargi da cin hanci da rashawa.''











