Amurka ta ƙwace shafukan intanet masu alaƙa da gwamnatin Iran

Website screenshot that says the site has been seized
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Amurka ta ƙwace gomman shafukan labarai na intanet wadanda take tuhuma da yaɗa labaran ƙarya.

Yawancin shafukan sun bace daga inda aka san su ranar Talata, inda aka wallafa wani sako da ke bayyana wa masu karatu cewa Amurka "ta ƙwace su" - kuma akwai tambarin 'yan sandan FBI da na ma'aikatar ciniki.

Cikin shafukan da aka kwace akwai na tashar talabijin ta Press TV da al-Masirah TV wanda 'yan Houthin Yemen ke gudanarwa.

Wannan matakin na zuwa ne yayin da dangantaka tsakanin Amurka da Iran ke kara tsami kan batun sake sabunta yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta ce ta kwace shafukan intanet 33 da kungiyar ma'aikatar Rediyo da Talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke gudanar da su, akwai kuma wasu uku da Hezbollah ke iko da su inji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Masu ziyartar shafukan sun kasa samunsu ranar Talata, inda wani sako daa ka wallafa a shafin al-Alam ke cewa: "Gwamnatin Amurka ta kwace wannan shafi na intanet na alalamtv.net... karkashin wani mataki da Ofishin Kwadago da Tsaro da Ofishin Cikikayya da Kasashen Waje da kuma Hukumar FBI su ka dauka."

Irin wadannan sakonnin aka wallafa a shafukan Press TV, wadda tasha ce da ke wallafa labarai da harshen Turanci wadda kuma gwamnatin Iran ke mara wa baya. Akwai kuma Al Alam TV wadda takwarar Press TV ce sai dai da Larabci ta ke wallafa na ta labaran. Sai kuma Lualua TV da ke watsa shirye-shiryensa daga Birtaniya a harshen Larabci amma mallakin gwamnati bahrain ne.

Iran na mara wa 'yan Houthin Yemen baya, kuma dodewar ta shafi wani shafin intanet na tashar talabijin din mai suna almasirah.net.

Amma yawancin kafofin yada labaran sun sake bayyana a intanet jim kadan bayan rufe sun da aka yi ta hanyar amfani da wasu sabbin adireshin intanet.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A watan Oktoba, Amurka ta kwace wasu shafuka 92 da ta ce Iran na amfani da su wajen yada labaran karya.

Gwamnatin Iran ba ta ce uffan ba a hukumance kan wannan matakin na Amurka, amma kafofin yada labarai a cikin kasar sun tuhumi Amurkar da kokarin rufe bakin Iran.

"Shin wannan ba wata lama ba ce na tsarin 'yancin fadin albarkacin baki samfurin Amurka, wanda idan Washington DC ba ta ji dadin abin da ka ke cewa ba, sai kawai a kwace shafinka na intanet?", inji wani sako na Twitter da Marzieh Hashemi, wani mai gabatar da shirye-shirye a tashar Press TV ya wallafa.