Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan bindiga sun tilasta wa mutane tserewa daga wasu garuruwan jihar Neja
Mazauna wasu yankuna na jihar Neja da ke arewacin Najeriya na ci gaba da tserewa daga gidajensu zuwa 'tudun-mun-tsira' sakamakon fargabar hare-haren 'yan bindiga.
Jama'ar garin Galadiman Kogo na karamar hukumar Shiroro sun tsere zuwa wasu garuruwa, bisa tsoron hare-haren 'yan bindiga bayan da aka janye wata tawagar jami'an tsaron da ke gudanar da sintiri a garin.
Kaurace wa garin da jama'arsa suka yi dai ta haddasa asara mai dimbin yawa ga manoma da masu gudanar da sauran sana'o'i.
Sai dai gwamnnatin jihar ta Neja, ta ce ana shirin kaddamar da wasu matakan tsaro masu inganci na dindindin a yankin da ma sauran sassan jihar da ke fama da matsalar tsaro.
Yanzu haka dai illahirin garin na Galadiman Kogo a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, ya koma kusan kamar kufai, a cewar wani mutumin garin mai suna Mubarak Danladi:
"Mun gudu mun tsere, wasu sun tafi garuruwa maƙwabta, wasu kuma birnin Minna suka gudu, wurare da dama, saboda barayin sun ajiye doka duk lokacin da jami'an tsaro zasu bar garin sai sun kawo hari musamman a Galadiman Kogo, su na zuwa wai mu yi sulhu da su, mu kuma mun ki amincewa da hakan shi ya sa wannan karon muka tsere daga garin," in ji shi.
Mubarak ya kara da cewa sun kwashe shekaru uku suna fama da wannan matsala ta hare-haren 'yan bindiga a yankin, har sai da aka kai masu jami'an tsaro a 'yan watannin da suka gabata, sannan suka dan sami sauki.
Sannan ɓarayin su na fasa shaguna su na sace kayan abinci da duk abin da ya ke da daraja kama daga na kayan abinci zuwa na bukatun yau da kullum.
Labarin halin da mutanen garin na Galadiman Kogo ke ciki dai, ya isa kunne gwamnatin jihar Nejar, kuma Ahmad Ibrahim Matane, sakataren gwamnatin jihar, ya ce ana kokarin kaddamar da wani shiri mai dorewa, don magance matsalar tsaron haihata-haihata.
Masu sharhi kan al'amuran tsaro dai na ganin matsalar tsaro tana ci gaba da zame wa gwamnatocin jihohi wani kulli gagara kunta, domin haka, sai gwamnatin tarayya ta kara zage damtse wajen murkushe matsalar.