Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Iran: Ebrahim Raisi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa
Shugabannin Turkiyya da Syria sun aika da saƙon taya murna ga Ebrahim Raisi kan nasarar lashe zaɓen Iran na shugaban ƙasa.
A cikin saƙonsa na taya murna, Shugaban Syria Bashar al-Assad ya ce yana fatan ƙarfafa danganta da gwamnatin Iran.
A nasa saƙon kuma, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bayan taya Ebrahim Raisi murna ya ce yana fatan sakamakon zaɓen zai kasance alheri ga mutanen aminiyar ƙasarsa.
"Ina mai bayyana cewa a shirye nake na bayar da hadin kai ga gwamnatinka domin kara karfafa dangantaka tsakanin kasashenmu," in ji shugaban Turkiyya.
Mai tsaurin ra'ayi Ebrahim Raisi ya lashe kujerar shugaban ƙasa ce a zaɓen da ake kallo a matsayin wanda aka shirya shi domin ya samu nasara.
Ya gode wa Iraniyawa bisa goyon bayan da suka ba shi bayan ya lashe kashi 62 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Mista Raisi mai shekara 60, shi ne aƙalin alƙalan Iran wanda ke da tsattsauran ra'ayoyi. Tuni Amurka ta saka masa takunkumi sannan kuma ana alaƙanta shi da hukunce-hukuncen da aka yanke wa 'yan adawar siyasa.
Muƙamin shugaban ƙasa ne na biyu mafi girma a Iran bayan shugaban addini.
Za a rantsar da Mista Raisi a farkon watan Agusta, wanda zai zama mai tasiri matuƙa game da muradin ƙasar na cikin gida da kuma na ƙasashen waje.
Sai dai a tsarin siyasar Iran, shugaban addini, Ayatollah Ali Khamenei, shi ne babban shugaba kuma sai da amincewarsa za a iya ɗaukar kowane irin mataki.
Tuni manyan abokan hamayyarsa a takarar shugaban kasa suka taya shi murna.
An hana masu da'awar sauyi tsayawa takara, kuma kusan duk waɗanda aka amince su tsaya takara sun kasance masu tsattsauran ra'ayi.
Masu sharhi sun ce tuni aka tsara yadda Raisi zai yi nasara.
Ya shafe shekaru yana taka rawa a kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kuma yana da kusanci da Jagoran Kasar, Ayatollah Ali Khamenei, kuma ya kasance babban mai sukar kasashen Yammaci.
Wane ne Ebrahim Raisi?
Mr Raisi shi ne babban alƙali kuma mai ra'ayin riƙau ne.
Yana cikin waɗanda Amurka ta ƙaƙabawa takunkumi.
Malamin, mai shekara 60, ya shafe rayuwarsa a matsayin mai gabatar da ƙara.
A 2019 aka naɗa shi babban alƙali, shekaru biyu bayan Rouhani ya doke shi a zaɓen shugaban ƙasa.
Mai tsananin biyayya ne ga shugabannin da ke mulki a Iran, ana ganin Raisi a matsayin wanda zai gaji Ayatollah Khamenei a matsayin babban jagoran kasar.
Raisi ya gabatar da kansa a matsayin mutumin da ya fi dacewa ya yaƙi cin hanci da rashawa da kuma magance matsalolin tattalin arzikin Iran.
Ya yi alƙawarin magance rashin aikin yi da kuma ƙoƙarin cire takunkumin Amurka wanda ya jefa Iran cikin matsalar tattalin arzikin.
Sai dai Iraniyawa da yawa da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam na bayyana damuwa kan rawar da ya taka wajen kashe fursunoni a shekarun 1980.
Amma ba ta taɓa amincewa da kisan ba kuma Raisi bai taɓa bayani ba kan zargin da ake masa ba.