June 12: Sauya ranar bai kawo karshen gwagwarmayar dimokradiyya ba a Najeriya, in ji masana

A ranar Asabar Najeriya ke bikin cika shekara 22 da komawar kasar kan turbar dimokradiyya, inda mahukunta da ƴan ƙasa suke kididdigar nasarori da kuma kalubalen ƙasar.

Wannan kusan shi ne karon farko da ake bikin a wannan rana tun bayan sauya ranar bikin daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni da gwamnatin kasar ta yi a shekarar da ta gabata.

Bikin na bana na zuwa ne a lokacin da kasar take fama da dimbin matsaloli musamman na rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki.

Kungiyoyi da dama sun ce za su fito domin gudanar da zanga-zanga a ranar ta yau.

Masana kan harkokin siyasa kamar Malam Kabiru Sa'id Sufi da ke koyarwa a Kwalajen Ilimi da Share Fagen Shiga Jami'a a Kano, ya shaida wa BBC cewa bikin na bana zai kasance daban da wadanda aka saba yi saboda karon farko ke nan da ake bikin a ranar 12 ga watan Yuni.

Da yake tsokaci kan wasu ƴan kasar da suka shirya yin zanga-zanga, Malam Sufi ya ce mutanen suna ganin kamar wata dama ce da za su fita domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda al'amura suke tafiya a gwamnatin dimokradiyya.

"Yana nuna cewa a gurinsu har yanzu gwagwarmaya bata kare ba duk da cewa an samar da tartibiyar dimokradiyya," in ji Kabiru Sufi.

Ya ce koken wannan ɓangare da ke zanga-zanga na da nasaba da zaɓen da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda ake ganin cewa akwai yiwuwar ɗaya daga cikin yan takarar Cif MKO Abiola age ganin kamar zai iya lashe zaben wanda kuma ana tsaka da zaben ne gwamnatin soji a lokacin ta yi amfani da kotu da ta ba da izinin a dakatar da zaben.

"Tun daga ranar su kuma yan gwagwarmayar dimokradiyya suka dauki ranar a matsayin ranar da suke gwagwarmaya har sai da a bara, gwamnati ta amince da ranar a matsayin ranar dimokradiyya abin da ake ganin watakila zai kawo karshen gwagwarmayar amma bai kawo ba," in ji masanin.

Kabiru Sufi ya kara da cewa da alamu akwai wata bukata ta daban - waccan gwagwarmayar ya kamata a ce abubuwan da aka yi sun kawo karshenta.

"Yanzu wannan wasu ne suka dauke ta (ranar) a matsayin ranar da suke ganin za su nuna tasu bijirewar da abubuwan da basu gamsu da su ba a kan abin da gwamnati take a kai yanzu ba, amma ba irin gwagwarmayar da aka yi ba ce daga 1993 har zuwa watakila shekarar da ta gabata," a cewarsa.