Janar Farouk Yahaya: Babban Hafsa ya yi garambawul ga rundunar sojin kasa ta Najeriya

Babban Hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya Janar Farouk Yahaya ya yi garambawul ga manyan jami'an rundunar tasa karon farko tun bayan da aka nada shi a kan mukamin a watan jiya.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Mohamed Yarima ya fitar ranar Alhamis ta ce an yi wa manyan jami'an rundunar sauye-sauyen wurin aiki ne domin cika burin babban hafsan rundunar "wajen samar da sojin Najeriya da ke shirye domin sauke nauyin da aka dora masa game da tsaron kasar."

Manyan sojojin da garambawul din ya shafa sun hada da Manjo Janar FO Omoigui daga Hedikwatar rundunar Hadin Kai zuwa Cibiyar Land Forces Simulation Centre ta Najeriya inda aka nada shi a matsayin babban daraktanta.

Sai kuma Manjo Janar CG Musa daga Nigerian Army Resource Centre zuwa Hedikwatar rundunar Hadin Kai kuma aka nada shi a matsayin Kwamandan rundunar.

Shi ma Manj Janar OR Aiyenigba an sauya masa wurin aiki daga Hedikwatar Tsaron Najeriya zuwa Hedikwatar Rundunar Sojin da ke aikin 'yan sanda inda aka nada shi a matsayin Shugaban Soji, yayin da Manjo Janar IM Jallo ya samu sauyin wurin aiki daga Defence Space Administration zuwa Hedikwatar rundunar Hadin Kai kuma aka nada shi a matsayin mataimakin Kwamanda na 1.

Wasu manyan sojin da garambawul din ya shafa sun hada da Birgediya Janar NU Muktar daga Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Islamabad zuwa ofishin Babban hafsan rundunar sojin kasa inda aka nada shi a matsayin Daraktan Sayo kayan soji, yayin da shi kuma Birgediya Janar O Nwachukwu aka sauya masa aiki daga Rundunar Tsaro (Kakakin rundunar) zuwa rundunar sojin kasa inda ya zama kakakinta.

Shi kuwa Birgediya Janar AE Abubakar daga Sashen Bayar da Horo da Tsare-Tsare (wanda aka soke) ya koma Hedikwatar Birged ta 22 kuma an nada shi a matsayin Kwamanda, yayin da Birgediya Janar KO Ukandu daga ofishin babban hafsan rundunar sojin kasa (Darakatan Sayo kayayyaki) zuwa Kwalejin Tsaro ta Kasa kuma aka nada shi a matsayin Daraktan Ma'aikata.

Kazalika an sauya wurin aikin Birgediya Janar IB Abubakar daga Makarantar Koyon aiki da makamai masu sulki ta sojin Najeriya zuwa Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa a sashen tsare-tsaren sojin kasa inda ya zama mataimakin daraktan tsare-tsare.

Shi ma Birgediya Janar AM Umar daga Kwalejin Horon Yaki ta Najeriya ya koma ofishin babban hafsan rundunar sojin kasa inda aka nada shi a matsayin shugaban ma'aikata na babban hafsan sojin kasa, sai kuma Birgediya Janar AJS Gulani daga Makarantar Koyon aiki da makamai masu sulki ta Rundunar Sojin kasa zuwa Hedikwatar Birged ta 24 inda ya zama Kwamanda.

Sauran jami'an sojin da aka sauya wa wuraren aiki sun hada da Kanar KE Inyang daga Hedikwatar tsare-tsare ta rundunar sojin kasa zuwa ofishin babban hafsan sojin kasa inda ya zama mataimakin fannin soji na babban hafsan sojin kasa.

Kanar OO Braimah daga Hedikwatar rundunar Hadin Kai zuwa ofishin jakadancin Najeriya da ke Islamabad inda aka nada shi a matsayin jami'in tsaro, yayin da Kanar IP Omoke daga ofishin babban hafsan sojin kasa zuwa Rundunar Tsaron sirri inda aka nada shi a matsayin mataimakin darakta kan hulda da kasashen waje (rundunar sojin kasa).