Hotunan Afirka na mako daga 4 zuwa 10 ga watan Yunin 2021

Mun zabo muku wasu fitattun hotunan Afirka na wannan makon:

Mace da jikinta sun kunna kyandir

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Lokacin da aka dauke wutar lantarki a Afirka ta Kudu ranar Laraba, Cecilia Nkosi ta rika hira da jikanta Samangaliso a gidansu da ke Soweto.
Wani yaro yana leka taga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Talata, kananan yara sun rika lekawa ta tagar cocin Minya Governorate a wani bangare na bikin da Kiristoci mabiya darikar Kibdawa suke yi domin tunawa da ranar "tafiya zuwa Masar".
Masu zanga-zanga suna rike da kwalayen da aka ruba " Shugaban kasa Assimi, firaiminista Choguel".

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu goyon bayan kungiyar M5 ta kasar Mali wadda ta taimaka wajen kifar da gwamnatin Shugaba Boubacar Keïta shekara daya da ta wuce sun sake fitowa kan tituna domin tunawa da ranar. Gwamnatin sojin kasar ta nada Choguel Maïga, mutumin da ya jagoranci M5, a matsayin firaiminista gabanin zaben da suka yi alkawarin gudanarwa a shekara mai zuwa.
A woman and a man sit on pile of picked maize.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Talata manoman masara Catherine da Desderioa Mubaiwa sun shaya ta a Zimbabwe, inda gwamnatin kasar ta hana shigo da hatsi sakamakon kakar da aka samu mai kyau a kasar.
'Yan kungiyar makada suna hutawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kazalika a ranar ta Talata a babban birnin Ethiopia wato Addis Ababa, masu kida sun zauna sun huta kafin babban bikin da aka yi na tunawa da zagayowar ranar da a karon farko kasar ta sayar da lasisin kamfanonin sadarwa ga kamfanoni masu zaman kansu. A ranar ce babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa yankin Tigray da yaki ya ɗaiɗaita yana "fuskantar faɗawa cikin fari".
A stage prop stands on the stage floor.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani gunki da aka yi baje-kolinsa lokacin wani shiri mai taken Iyagbon's Mirror...
Cast members practise a scene.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu shirya fina-finai a Najeriya sun yi fim game da "tasirin mulkin mallaka" a kan "galibin kayan tarihin Afirka" wadanda aka "saya, gano ko kuma sacewa kuma aka yi baje-kolinsu" a Turai, inda suke duba yadda za su sake fasalin tsarin na dawo da "karfin" da kayan tarihin suke da shi a baya
A man walks through shafts of light and shadow.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum yana wucewa ta Circa Gallery da ke Johannesburg, Afirka ta Kudu, ranar Alhamis
A women knits a blanket while she sits among hundreds of other blankets.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Har wa yau a birnin na Johannesburg a ranar Laraba, masaka sun gudanar da wani aiki na saka dubban barguna ga mutane masu bukata a watannin da ake tsananin sanyi.
A Masar ranar Litinin, wannan matar tana saka kwando da robobin da ake sake sarrafawa da aka bebo daga Kogin Nilu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Masar ranar Litinin, wannan matar tana saka kwando da robobin da ake sake sarrafawa da aka bebo daga Kogin Nilu.
A can gabar tekun Tunisia, ranar Juma'a wani mai rajin kare muhalli yana cire ciyayi domin inganta muhalli

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A can gabar tekun Tunisia, ranar Juma'a wani mai rajin kare muhalli yana cire ciyayi domin inganta muhalli
Ita ma kungiyar Canaan Riverside Green Peace da ke Kenya tana kokarin fitar da datti daga cikin Nairobi River ranar Asabar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ita ma kungiyar Canaan Riverside Green Peace da ke Kenya tana kokarin fitar da datti daga cikin Nairobi River ranar Asabar.
People sit inside a bus.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bayan tsaunin Nyiragongo ya yi aman wuta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, mutanen da ke zaune a gefensa da ma yankunan da ke kusa da shi ba su da zabin da ya wuce su tsere daga yankin. Fasinjojin da ke cikin wannan motar ranar Talata suna komawa gidajensu da ke Goma.
Wani mutum zaune a wajen shagonsa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kuma ranar Lahadi a Liberia, wani mutum yana zaune a kan a kofar shagonsa a kasuwar Gobachop da ke Monrovia, babban birnin kasar.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka