Abin da ya sa 'yan sanda suka hana makiyaya shiga Kano sai da izini

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yan sanda a Kano da ke arewacin Najeriya ta ce dukkan Fulani makiyayan da za su shigo jihar sai sun sami takardar izini daga kwamishinan 'yan sandan jihar da suka baro.
Kwamishinan 'yan Sandan jihar Sama'ila Dikko ya ce duk Bafilatanin da ba shi da takardar izini daga 'yan sandan garin da ya fito ba, sai sun zurfafa bincike kafin su bar shi ya shiga jihar Kanon.
Sama'ila Dikko ya kara da cewa, fulanin sai sun nuna takardar shaida daga shugabanninsu, sannan ko da makiyayi ba shi da takardar za su yi bincike a kansa idan ba su gamsu da bayanan aka samu a kansa ba, to sai dai ya koma inda ya fito.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da da samun karuwar fulanin da ke kwararowa cikin kanana huikumomin da ke makotaka da Jihohin Kaduna, Katsina da Jigawa.
''Mun fahimci cewa fulanin da za su shiga jihar Adamawa su na shiga da takardu daga shugabanninsu na Fulani, sukan ba su takardar cewa saboda hali na kiwo su na neman inda za su fi samun ciyawa da ruwa da sauransu.
"Wasu kuma su na karbar takardar ne daga wajen 'yan sanda saboda sha'anin tsaro a kuma tabbatar da cewa ba ɓarayi ba ne.
"Shi ya sa muma muka dauki wannan matakin domin sanin cewa ba barayin shanu ko 'yan ta'adda ne masu aikata laifi ba ne, domin magance matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya,'' in ji Sama'ila Dikko.
Jami'an tsaron sun zauna da shugabainin Fulanin wadannan jihohi da kuma na cikin Kano don sanar da su halin da ake ciki tare da neman hadin kansu domin ganin an tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar ta Kano.
Karuwar rashin zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da mazauna kudancin Najeriya, na daga cikin dalilan da ya sa suke yin ƙaura zuwa arewacin kasar.











