Boko Haram: Sojoji sun ce sun kama 'yan kungiyar 13 a Kano

Boko Haram sun soma kaddamar da hare-hare a 2009

Asalin hoton, Boko Haram

Bayanan hoto, Boko Haram sun soma kaddamar da hare-hare a 2009
Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar sojojin Najeriya ta yi ikirarin kama mutanen da take zargi da kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram a jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar, Njoko Irabor, wanda ya tabbatar wa BBC hakan, ya ce sun kama mutanen ne a wani masallaci da ke unguwar Hotoro a cikin birnin Kano ranar Asabar.

Ya ce sun kamo mutanen ne a wani samame da suka kai masallacin bayan samun bayanan sirri a kansu.

A cewarsa, suna ci gaba da faɗaɗa bincike da tattara bayanan sirri da zummar inganta tsaro a jihar ta Kano.

Sai dai a yammacin ranar Lahadi rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwa a shafinta na Twitter inda ta ce ta kama mayakan Boko Haram 13 a ranar Asabar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Sanarwar sojojin ta ce za ta kara fadada komarta wajen zaliko muggan mutanen da ke fake wa cikin jama'a da manufar cutar da su.

Ta kuma nemi mutanen yankin na Hotoro da su ci gaba da al'amuransu na rayuwa tare da sanya ido akan duk wata bakuwar fuska ko kuma bakon motsin da basu gamsu da shi ba.

Rahotanni sun ce wannan kamen ya tayar da hankulan mazauna wasu yankunan birnin na Kano.

Wannan ne karon farko cikin lokaci mai tsawo da hukumomi suke sanar da kama wadanda ake zargi da kasancewa 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram a jihar Kano.

A shekarun baya, birnin na Kano ya yi fama da hare-hare na mayakan kungiyar, wadanda suka taba tashin bam a babban masallacin da ke kofar gidan Sarkin Kano da kuma wasu wurare.

Rundunar sojin ta kama mutanen ne a yayin da kungiyar Boko Haram ke matsa kai hare-hare musamman a Arewa maso gabashin kasar.

Presentational grey line
Bayanan bidiyo, Abdussalami Abubakar: Tsohon shugaban Najeriya ya koka kan matsalar tsaro

A watan jiya mayakan kungiyar sun kai hari garin Geidam da ke jihar Yobe inda suka kashe mutane da dama sannan suka tilasta wa daruruwa tserewa daga gidajensu.

Baya ga garin na Geidam, mayakan Boko Haram sun kai hari kan sansanin sojin Najeriya da ke garin Mainok na jihar Borno inda rundunar soji ta tabbatar da cewa sun kashe sojoji bakwai da kwamandansu guda daya.

Sai dai rahotanni sun ce mayakan na Boko Haram, wadanda ke cikin manyan motocin yaki lokacin da suka kai harin, sun kashe fiye da sojoji 30.

Kazalika mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kafa tuta a kananan hukumomi biyu na jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, kamar yadda gwamnan jihar Sani Bello, ya shaida wa manema labarai a watan jiya.

Masu sharhi kan lamuran tsaro irin su Barista Audu Bulama Bukarti sun ce mayakan Boko Haram sun matsa kai hari a baya bayan nan ne saboda a ganinsu hakan zai sa su samu karin lada daga wurin Allah a lokacin watan Ramadan.

Presentational grey line