Yadda ma'aikatan da Gwamna El-Rufa'i ya kora daga aiki 'suka fada cikin tasku'

Nasir El-Rufa'i

Asalin hoton, Kaduna Govt

Bayanan hoto, Malam Nasiru El-Rufa'i ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe kan maganar sallamar ma'aikata

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, wasu ma'aikata da gwamnatin Nasir El-Rufa'I ta sallama daga aiki na kukan cewa sun fada cikin mawuyacin hali tun bayan da gwamnatin jihar ta sallame su daga aiki.

Ma'aikatan sun shaida wa BBC cewa abin da za su ciyar da iyalansu ma na fin ƙarfinsu.

Tun a shekara ta 2017 aka yi musu ritayar dole, inda suka yi zargin cewa ba a biya su haƙƙoƙinsu ba. Sai dai gwamnatin jihar ta ce ta yi musu tayin koya musu sana'ar noma amma da dama sun yi biris da ita.

Kazalika, sun ce an katse musu rayuwa da su da iyalansu, kasancewar abin da suke taimaka wa wasu da shi ya fi ƙarfinsu, kasancewar ba su shirya wa sabuwar rayuwar da suka samu kansu a ciki ba.

"Ina nadamar shiga aikin koyarwa'

Cikin wadanda aka yi wa irin wannan sallamar har da malaman makaranta.

Malam Ahmed Mato Lere ya ce ya shiga halin tasku bayan an yi masa ritaya, har ta kai ga yana nadamar rungumar koyarwa a matsayin sana'a.

"Na shiga cikin wani yanayi. Nakan kwanta da matata ina tunanin abin da zan karya da safe," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "Ana bi na bashi na kuɗin makarantar yara. An nemi ma a kore su amma ina zuwa ina bayar da haƙuri ana ƙyale su.

"Na yi nadama tsakanina da Allah cewa da na san zan tsinci kaina a irin wannan lamari wallahi tallahi da ban yi sana'ar koyarwa ba."

Bayanan bidiyo, Yadda ta kaya tsakanin NLC da El-Rufa'i a yajin aikin Kaduna

'Ina da shekara 48 aka yi mani ritayar dole'

Hajiya Hadiza Ahmed ma'aikaciyar ƙaramar hukuma ce da aka yi wa ritaya a matakin albashi na 13.

"An ce akwai tsari da gwamnati ta fito da shi cewa duk waɗanda aka sallama daga 2017 idan ya cika shekara 50 za a fara ba shi fansho, idan kuma ba ka cika 50 ba za a ba ka fansho ba.

"Idan kuma ka fara karɓar fansho ba za a ba ka giratuti ba [kuɗin sallamar ma'aikaci," a cewar Hadiza.

Ta ƙara da cewa naira 8,000 ake ba ta a matsayin fansho.

Wannan layi ne

'Ba a fara biyana fansho ba har yanzu'

Shi kuwa Malam Abubakar Muhammad cewa ya yi yana rayuwa ne da ikon Allah, saboda kudin fanshon ma bai yi katarin samu ba.

Ya ce: "Rayuwa ta yi tsauri gaskiya. Mutum na gidan haya, ba abin da za a ci, ga makarantar yara, sannan mutum bai iya kowace sana'a ba sai aikin nan, aka zo aka kore ka ba tare da biyanka haƙƙinka ba.

"Islamiyya nan idan aka koro yaro sai dai na je na roƙi arziki, kuma idan lokacin da suka ba ni ya cika ban biya ba su sake koro shi. A haka ake rayuwar."

Da wakilin BBC Ibrahim Isa ya tambaye shi ko nawa ake ba shi kuɗin fansho, sai ya ce: "Ai ba a ma fara ba ni kuɗin fanshon ba ballantana na san nawa ne."

Karin labarai masu alaƙa

Wannan layi ne

Ta'addanci ne a kori mutum daga aiki kuma a hana shi haƙƙinsa - ASG

Irin waɗannan mutanen da aka sallama na cikin rukunin ma'aikatan da ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta tsaya kai-da-fata cewa sai gwamnatin jihar Kadunan ta duba al'amarinsu, tana zargin cewa ba ta bi dokar ƙwadago ba wajen raba su da aikin.

Su ma ƙungiyoyin farar-hula suna mara wa ɓangaren ma'aikatan baya.

Comrade Musa Jika, jami'i ne a kungiyar Amnesty Support Group kuma ya kwatanta halin da waɗanda aka kora suke ciki da cewa "ta'addanci ne".

"Hakan na iya sa mutum tunanin iri daban-daban wanda zai ma iya kasa bai wa ƴaƴansa tarbiyya, kuma duk a kan albashi iyalin suka dogara.

Wannan layi ne

Me El-Rufa'i ya ce?

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna, kamar yadda Gwamna Mallam Nasiru El-Rufa'i ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe kan maganar sallamar ma'aikata.

"Ba zamu zama jihar da abinda take yi kadai shi ne biyan albashin ma'aikatan gwamnati ba, kuma ba wani matsai da zai sa mu canza wannan matsayar. Zamu rahge ma'aikata da kuma masu mukaman gwamnati na siyasa.

"A 2017 mun yi niyyar ba da gonaki ga ma'aikata da malaman makaranta da muka sallama aiki don su yi sanaar noma amma kadan daga ciki ne suka nuna son karba. wadannan filaye na noma suna nan har yanzu tare da ba su kananan kudade don yin jarin kasuwanci

Sakamakon wannan takaddama da ake yi a kan sallamar ma`aikata, sai da kungiyar kwadago ta kasa ta jagoranci wani yajin aiki na gargadi, lamarin da ya durkusar da harkokin tattalin arziki a jihar Kaduna.

Ko da yake, ana tsaka da yajin aikin ne ma`aikatar kwadago ta kasa ta shiga tsakani.

A yanzu dai an kafa wani kwamiti da ke duba hanyar sasanta bangarori biyun.

Wannan layi ne