Hotunan yadda mutane ke sayen abincin azumi a kasashen duniya

Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images/AFP

Bayanan hoto, Itatuwan Habal da kayan yaji a kasarwar Dubai da ke Hadaddiyar Daular Laraba a ranar 12 ga watan Afrilu 2021, lokacin da Musulmai ke daf da fara Azumin Watan Ramadana
Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images/AFP

Bayanan hoto, 'Yan kasar Oman na sayan kayan abinci a kasuwar Mawaleh da ke Muscat babban birnin kasar yayin da ake shirin fara Azumin Watan Ramadana a fadin duniya, an dauki hoton ne a ranar 12 ga watan Afrilun 2021.
Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images/AFP

Bayanan hoto, Wani dattijo na sayar da kayan itatuwa da sauran kayan marmari a bakin shagonsa da ke Hebron tsohon birnin da Isra'ila ta mamaye a yankin Gabar Yamma da Kogin Jodan, wani shirye-shirye da Musulmai ke yi a fadin duniya na Azumin Ramadana da za a fara a wannan makon. An dauki hoton a ranar 12 ga watan Afrilu 2021
Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu yara Musulmai na karbar kayan tallafi a ranar 11 ga watan Afrilu 2021, dab da za a fara Azumin Ramadana, an dauki hoton ne a yankin kudancin lardin Pattani na Thailand.
ramadana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan kabilar Aceh sun yi dafifi a kasuwa suna sayan kayayyaki a wani mataki na tunkarar Azumin watan Ramadana da za a fara a wannan makon a fadin duniya. Babbar kasuwar ta saba karbar mutane da suke sayayya a cikinta a lokutan Ramadana da karamar Salla da kuma babba. ranar 12 ga watan Afrilu a ka dauki hoton kasuwar
Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata 'Yan kabilar Aceh na sayan nama a kasuwa. Babbar kasuwar ta saba karbar mutane da suke sayayya a cikinta a lokutan Ramadana da karamar Salla da kuma babba. ranar 12 ga watan Afrilu a ka dauki hoton kasuwar
Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane a jere a layin sayen sikari kan farashin gwamnati a Alahore, a wani mataki na shirin samar da tallafi da gwamnatin yankin ta yi a ranar 11 ga watan Afrilu
Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikatan gidauniyar Al-Khidmat na shirya kayan agajin a jikin jakankuna domin rabawa bayin a Islamabad Allah lokacin da ake tunkarar Azumin watan Ramadana a ranar 11 ga watan Afrilu 2021.
Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata mabukaciya ta karbi kayan agajin watan Ramadana a Islambad na Pakistan, wanda asar Hadaddiyar Daular Larabawa ta raba, a shirye-shirye da ake yi na fara Azumin Watan Ramadana a ranar 12 ga watan Afrilu 2021.
Getty Images/AFP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mabukata a lokacin da suka shiga layi suna karbar kayan agaji a kofar ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa da ke Isalamabad a ranar 12 ga watan Afrilu 2021, sai da aka tabbatar da ba da tazara da kuma sanya takunkumi a fuskanr ko wanne mabukaci
Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu sayayya a kasuwar Istambul da ke Turkiyya sanye da takunkumi a ranar 09 ga watan Afrilu 2021. A ranar ne aka sanar da mutum 55,000 sun kamu da cutar cikin kwana guda adadin da ba a taba samu ba tun bayan bullar cutar a kasar. A kwanan nan ne aka bayar da umarnin janye dokar hana zirga-zirga da aka sanya a kasar tare da bude shagunan sayar da abinci da kuma shayi, amma duk da haka akwai fargabar cewa bullar za ta iya ci gaba da yaduwa lokacin murnar kama azumi watan Ramadana.
ramadana

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Wasu 'yan kasar Murtaniya lokacin da suke karbar kayan agaji daga wasu kungiyoyin kasar Turkiyya gabanin watan Azumin Ramadana a ranar 5 ga watan Afrilu 2021.
Nan kuma wasu mabuƙata ne ke karbar tallafin azumi a kasar Chadi wanda gwamnatin Saudiyya ta aika

Asalin hoton, Saudi Gazette

Bayanan hoto, Nan kuma wasu mabuƙata ne ke karbar tallafin azumi a kasar Chadi wanda gwamnatin Saudiyya ta aika.

Dukkan hotunan haƙƙin mallakar Getty