Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tattalin arziƙi: Matakan da aka bi wurin ceto tattalin arziƙin Najeriya daga masassara
Ministar Kudi da Tsare-tsaren tattalin Arzikin Kasa, Zainab Ahmed Shamsuna, ta yi karin haske kan ficewar Najeriya daga matsalar koma-bayan tattalin arziki da ta shiga sakamakon annobar cutar korona da kuma faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya.
Sai dai ta ce ko da ya ke tattalin arzikin ya dan bunkasa da kashi sufili da digo daya cikin dari 0.1% a karshen shekarar da ya gabata, to amma ci gaban bai kai yadda za a iya miƙe kafa a sakankance ba.
Ministar ta kuma ƙara da cewa farfadowa da yanzu darajar danyen man fetur ke yi, da kuma lamunin biliyoyin dala daga Asusun Lamuni na Duniya da Bankin Duniya da kuma Bankin Raya Afirka a shekarar 2020, duka sun kasance wata kyakkyawar alama cewa tattalin arzikin zai ci gaba da farfadowa.
Bayan taron manema labaran a Fadar Shugaban Kasa, ministar ta yi wa wakilin BBC Ishaq Khalid karin bayanin kan matakan da aka bi domin ficewa daga matsalar koma-bayan tattalin arzikin.
Ta ce shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari da farko ya sa su rage wasu wuraren da za a yi amfani da kudi wadanda ba lallai ne sai an yi su a shekarar ta wuce ba.
Da hakan ya sa suka samu wasu kudi da aka yi amfani da su a fannin inganta kiwon lafiya da kuma taimaka wa al'ummar Najeriya da suka zama gajiyayyu.
Zainab Ahmed ta kuma ce mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar karamin kwamitin da aka zana tsarin da ake kira ''Economic Sustainability Plan'', wanda ya yi aikin gyara tattalin arzikin kasa na shekarar da ta wuce (2020).
Ya kuma ya bayar da umarnin cewa a tsara yadda za a yi a fitar da kasa daga cikin matsalar da ta shiga.
''Shi wannan tsari da aka yi ya danganta da aikin gona, yadda za a taimaka wa ƙananan da matsakaitan manoma a ba su kudi masu karamin ruwa domin su samu su ci gaba da aikinsu na noma," in ji ministar.
''Akwai kuma wasu tallafi da aka bai wa mutane da suke da kananan kamfanoni ko 'yan kasuwa don su kara jari.
"Kana akwai karkashin wadannan tsari na ''Economic Sustainability Plan' wanda da shi ne ya taimaka mana ya sa muka fita cikin wannan ƙangi,'' in ji ta.
Ministar ta kuma bayyana cewan an dauki mutane aiki wanda ko wace karamar hukuma an dauki mutum dubu daya, kuma ko wane minista cikin 'yan makonni da suka wuce ya je jiharsa don daukar ma'aikata.
Ta bangaren kananan kudaden tallafi kuwa in ji ministar, mutane sun zo duka an rarraba musu domin rage kaifin wahalhalun da suka shiga wanda annobar cutar korona ta haifar.