Lokaci huɗu da rundunar sojin saman Najeriya ta shiga makoki

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike bayan wani jirgin saman kasar ya rikito a Abuja babban birnin kasar.

Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce dukkanin mutum bakwai da ke cikin jirgin ne suka mutu a hatsarin.

Hukumomi sun ce jirgin samfurin King Air 350 ya samu matsalar na'ura a lokacin da yake kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Minna da ke jihar Neja dmin ceton mutum 42 ne da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.

Ba wannan ne karon farko da rundunar sojin saman Najeriya ta fada cikin jimami ba sakamakon wani ibtila'i da ya shafi jami'anta da ma fararen hula.

Jirgin saman soji ya kashe mutum bakwai a Abuja

Bari mu fara da hatsari na baya-bayan nan da ya faru ranar Lahadi, inda sojojin saman Najeriya suka mutu sakamakon hatsarin da jirginsu ya yi a kusa da garin Basa da ke babban birnin ƙasar, Abuja.

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce dukkanin mutum bakwai da ke cikin jirgin ne suka mutu a hatsarin.

Mutanen su ne: Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Kyaftin), Flight Lieutenant Henry Piyo (Matukin jirgin), Flying Officer Micheal Okpara (Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Warrant Officer Bassey Etim Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Sergeant Ugochukwu Oluka (Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Aircraftman Adewale Johnson (Jami'in jirgin sama).

Waɗanda suka gane wa idonsu sun faɗa wa BBC cewa sun ji ƙara mai ƙarfi kafin jirgin ya kama da wuta.

'Yan bindiga sun kashe sojojin sama da dama a Kaduna

A ranar 14 ga watan Fabrairun da muke ciki ne 'yan bindiga da ke yawan kai hare-hare a wasu jihohin arewacin Najeriya suka kashe jami'an rundunar sojin saman kasar a Unguwar Laya ta Birnin Gwari da ke Kaduna.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin sama Ibikunle Daramola ya fitar a wancan lokaci ta ce 'yan bindigar sun yi wa dakarun rundunar 271 ta sojin sama da ke aikin kakkabe bata-gari a yankin kwanton-bauna, inda suka kashe sojojin da bai bayyana adadinsu ba.

A cewarsa, wasu jami'an nasu sun samu raunuka sanadin kwanton-baunan.

Sai dai ya ce a nasu bangaren, sojojin sun kashe 'yan bindiga "fiye da 100."

Matuƙiyar jirgin yaƙin Najeriya Tolulope Arotile ta mutu

Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga cikin alhini a watan Yulin 2020 sakamakon mutuwar matuƙiyar jirgin yaƙinta a birnin Kaduna da ke arewacin kasar.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce binciken da suka gudanar da farko ya nuna cewa marigayiyar ta mutu ne sakamakon buguwa a kanta bayan da wasu da suka yi makarantar sakandare tare suka bugi motar da take ciki.

Rundunar ta yi wannan bayani ne sakamakon yadda mutane suka yi ta neman ƙarin bayani game da mutuwar Arotile.

Sanarwar da kakakin rundunar sojan saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce abin da ya faru shi ne ranar 14 ga watan Yuli da ƙarfe 10:00 na safe, Tolulope Arotile ta karbi wani kira daga abokin aikinta Flying Officer Perry Karimo, inda ya bukaci ta zo sansanin sojin sama na Kaduna don su tattauna yadda za su koma aiki Enugu.

A cewar sanarwar 'yar uwar marigayiyar ce mai suna Mrs Adegboye ta ɗauko ta a mota zuwa sansanin sojan don amsa kiran da aka yi mata.

Bayan Flying Officer Arotile ta isa sansanin ne sai ta saka wayarta caji a gidan wani Squadron Leader Alfa Ekele sannan ta wuce zuwa kasuwar bariki ta mammy market don a yi mata kwafin wasu takardu.

Bayan ta kammala za ta koma ne da ƙarfe 4:30 na yamma, sai wasu waɗanda suka yi makarantar sakandire tare su uku suka wuce a mota.

"Da suka hange ta sai suka koma da baya da sauri don su yi mata magana, lamarin da ya sa suka banke ta da mota ta baya, inda kanta ya bugu da gefen hanya sannan suka bi ta kanta" a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce nan take aka garzaya da Flying Officer Arotile zuwa asibitin sojojin sama na Kaduna.

Jirgin saman sojojin Nigeria ya kashe 'yan gudun hijira

A ranar 17 ga watan Janairun 2017 ne wani jirgin saman sojin Najeriya bisa kuskure ya jefa bam kan sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Rann a jihar Borno.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 115, cikinsu har da ma'aikata shida na kungiyar agaji ta Red Cross, sannan fiye da mutum 100 suka jikkata.

Sanarwar da rundunar sojin saman ta fitar bayan jefa bam din, ta ce ta yi zaton mayakan kungyar Boko Haram ne suka yi sansani a wurin.

Wannan lamari ya tayar da hankalin 'yan kasar da ma rundunar sojin saman, wacdda ta sha alwashin gudanar da bincike kan batun.