Abin da ya sa kotun Kano ta wanke matar da ake zargi da kashe ƴar aikinta

Mata

Asalin hoton, Getty Images

Wata kotun majistire a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta wanke wata mata Fatima Hamza daga zargin da ake yi mata na kisan ƴar aikinta.

A zaman kotun da ke unguwar Gyadi-gyadi, mai shari'a Ibrahim Khalil ya ce an sallami wadda ake karar ne saboda roƙon da lauyan gwamnati ya yi na a sallame ta saboda rashin ƙwararan hujjojin da za su tabbatar da laifin da ake tuhumarta da aikatawa.

Sannan ma'aikatar shari'a ta jihar Kano ta buƙaci kotun ta umarci kwamishinan yan sandan jihar Kano ya gudanar da bincike dangane da wasu ƴan jarida a jihar bisa bayar da bayanan ƙarya dangane da wannan alamari.

Rundunar yan sandan jihar Kano ce ta gurfanar da matar a gaban kotu tun a ranar 4 ga watan Fabrairu, bayan da kafofin watsa labarai a jihar suka rawaito cewa ta kashe yar aikinta Khadija Musa mai shekaru 19 a duniya.

Wannan al'amari ya janyo taƙaddama a Kano, tare da bijiro da damuwar da ake da ita kan yadda al'adar ɗaukar ƙananan yara a gidaje da sunan ƴan aikatau ke daɗa jefa yara da 'yan mata cikin uƙuba ta hanyar ci da guminsu.

Rahotanni sun ce 'yan gidan da take yi wa aikatau ne suka kai ta asibiti amma sai jami'an asibitin suka ƙi karɓar ta saboda babu rahoton 'yan sanda.

'Yan sanda sun ce bincikensu na farko-farko ya nuna cewar akwai tabo a gefen fuskar 'yar aikin da ta mutu sannan akwai ɗinki a wajen al'aurarta.

'Yan sandan sun ƙara da cewa mai gadi da wasu mazauna gidan da abin ya faru sun yi iƙirarin cewa muzuru ne ya yi sanadin mutuwar Khadija Musa lokacin da aka tambaye su.

Wakilin BBC a Kano ya ce batun ya yi matuƙar jan hankalin jama'a a birnin jim kaɗan bayan ɓullar muryar wata yarinya da ake jin tana iya zama shaida cikin lamarin, a wata kafar yaɗa labarai.

Muryar ta zargi uwar ɗakin Khadija Musa da gana wa marigayiyar azaba tare da zuba mata barkono a al'aura da dukanta da muciya a duk lokacin da ta yi mata wani laifi.

Sai dai a yanzu kotun majistiren ta ce shaidun da aka gabatar basu isa tabbatar da zargin da ake yi ba, a don haka ne ta wanke Fatima.