Junaidu Mohammed: Abubuwan da suka kamata ku sani game da marigayi dan siyarar

Junaidu Mohammed

Asalin hoton, OTHER

Lokacin karatu: Minti 1

A yau Juma'a ne aka yi jana'izar fitaccen dan siyasar nan na jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Dr Junaidu Mohammed.

An yi masa suttura ne a masallacin Alfurkan da ke Kano karkashin jagorancin limamin masallacin Sheikh Bashir Aliyu Umar.

Fitattacen dan siyasar a Jamhuriya ta biyu ya rasu ne da misalin karfe 9 na daren Alhamis a gidan sa da ke Titin Lamido Crescent a birnin Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya ta dan gajeran lokaci.

Ya rasu yana da shekara 73.

Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani game da dan siyarar.

Dan majalisar dokokin tarayya

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Kafin rasuwar sa, Dr Junaidu ya taba zama dan majalisa a Jamhuriya ta Biyu tsakanin 1979 zuwa 1983. Ya tsaya takara ne a a karkashin inuwar jam'iyyar PRP, kuma yana matukar mutunta Malam Aminu Kano, wanda suke da ra'ayi iri daya.

Likita

Junaidu Mohammed likita ne wanda ya yi karatu a Tsohuwar Tarayyar Soviet.

Fitaccen mai sukar gwamnati

Dr Junaidu Mohammed ya yi fice wajen sukar gwamnatocin Najeriya daban-daban a kan abin da ya kira rashin "mayar da hankali wajen inganta rayuwar 'yan kasar."

Kusan za a iya cewa babu gwamnatin da bai soka ba idan har ya ga tana kauce hanya, ciki har da gwamnatocin mulkin soji.

Ya bai wa Shugaba Buhari aron littafi

Dr. Junaidu Mohammed mutum ne mai matukar sha'awar karance-karance. A wata hira da ya yi da BBC Hausa, marigayin ya ce ya taba bai wa shugaban Najeriya Muhammad Buhari aron littafi domin shi ma ya karanta.