Tsohon shugaban hukumar kwastam ta Najeriya Dikko Inde ya rasu

Dikko Inde

Asalin hoton, TWITTER

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya sun tabbatar da mutuwar tsohon shugaban hukumar kwastam ta ƙasar Dikko Inde.

Wata majiya mai ƙarfi da ke da kusanci da mamacin ta tabbatar wa BBC cewa ya rasu ne a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Marigayin, wanda ɗan asalin garin Musawa ne na jihar Katsina, ya rasu yana da shekara 60.

Ya rasu ya bar mata ɗaya da yara uku, maza biyu da mace ɗaya.

An haifi Abdullahi Dikko Inde ranar 11 ga watan Mayun 1960. Ya kuma shiga aikin kwastam a shekarar 1988.

Ya zama shugaban hukumar kwastam a watan Agustan 2009 inda ya sauka a watan Agustan 2015.