Abin da Kanawa ke cewa kan yajin aikin masu A daidaita Sahu
Al'ummar birnin Kano a arewacin Najeriya suna ta bayyana irin yadda suke ji da kuma halin da aka shiga sakamakon yajin aikin da masu tuƙa babur mai ƙafa uku na a daidaita sahu suka fara a ranar Litinin.
Ɗalibai da ƴan kasuwa da ma'aikata sun shiga tasku a birnin na Kano yayin da aka wayi gari da yajin aikin.
Ra'ayoyin da mutanen birnin ke bayyanawa sun bambanta sosai.
Yayin da wasu ke kokawa kan halin taskun da rashin abin hawan ya sanya su ciki, wasu cewa suke ina ma dai Kanon ta zama haka babu cunkoson ababen hawa.
Sai dai masu kuka da wannan yajin aiki sun fi yawa, ganin cewa a daidaita sahu ne kaɗai hanyar sufurin da mafi rinjayen mazauna birnin ke amfani da shi.

Me mutane ke cewa?
A shafin Facebook al'ummar birnin da dama sun yi ta rubuce-rubuce kan abin da ke faruwa.
Masu kokawa kan hakan suna ganin ina talaka zai sa kansa a wannan yanayi tun da da a daidaita sahun suka dogara wajen zuwa nema.
Wasu kuwa musamman masu rajin kare muhalli ke ganin lokaci ya yi da jihar Kano za ta rage cunkoson da masu baburan ke kawowa a birnin, musamman don rage gurɓatar muhalli.
Ga dai abin da wasu ke cewa:

Asalin hoton, Widi-jalo Facebook
Abubakar Widi-jalo ya rubuta cewa: "A ganina akwai matsalar da ta fi ta naira 100 da gwamnatin Kano da masu a daidaita sahu suke rigima a kanta.
"Yawaitar da abin hawan a daidaita sahu ke yi a Kano abin duba ne. Zai iya jawo gagarumar matsalar muhalli da matsalolin lafiya idan ba a yi wani abu ba.
"Idan har ba a duba wannan lamari aka kuma tsara shi yadda ya kamata ba, to kuwa nan da shekara biyar mutum zai iya shafe sa'a biyar bai motsa daga wani takun zuwa wani ba saboda cunkoso.
"Kana yin magana kan sauye-sauye da rage yawan a daidata sahu a titunan Kano, al'amarin da ke zama matsala, za su ce kai ɗan jari hujja ne kuma maƙiyin talakawa. Allah ya sauwake."
Shi kuwa wani mai sharhi a Facebook ɗin Dr Ibrahim Musa ga abin da ya ce:

Asalin hoton, Ibrahim Musa Facebook
Shi ma Rabi'u Biyora cewa ya yi:

Asalin hoton, Biyora Facebook
Aliyu Isa Aliyu ya ce:

Asalin hoton, Aliyu Isa Facebook
Sai Sunusi Musa wanda ya bai wa gwamnati shawara da cewa:

Asalin hoton, Sunusi Musa Facebook
Taƙaddamar gwamnati da masu a daidaita sahu
Yajin aikin ya biyo bayan kukan da masu A saidata-sahun ke yi ne kan harajin naira 100 a kullum da gwamnatin jihar ta dawo da karɓa bayan ta dakatar da shi a kwanakin baya.
Shugaban hukumar sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan Agundi, ya faɗa wa BBC cewa harajin ba sabon abu ba ne.
"Da ma can haka ake biya kuma an dakatar da karɓa ne saboda zuwan annobar cutar korona," in ji shi.
Ya ƙara da cewa dokar da ta kafa hukumar KAROTA ce ta bayar da damar karɓar harajin.
Kazalika ya yi barazanar cewa yajin aikin bai damu gwamnati ba domin kuwa za ta iya kawo manyan motocin sufuri domin maye gurbin babura masu ƙafa uku a jihar.
Tuni rundunar 'ƴan sandan Jihar Kano ta kama mutum biyu da take zargi da shirya zanga-zangar da direbobin A daidaita-sahun suka yi niyyar yi a yau Litinin.
Tun farko dai direbobin sun shirya gudanar da zanga-zanga ne kafin daga baya 'yan sanda su haramta musu yin hakan.
Sufuri a Kano a shekarun baya
A baya akwai tasi-tasi mai fentin launin ɗorawa da shuɗi da bas-bas masu zirga da kuma achaɓa, amma tuni waɗannan ababen sufuri suka yi ƙaura daga titunan birnin, suka bar a daidaita sahu na cin kasuwarsu.
Duk da cewa babu wani bincike da ya nuna dalilin ɓacewar tasi da bas a titunan Kano, amma an san cewa hukumomi ne suka dakatar da yin acaɓa tun lokacin da rashin tsaro na hare-haren bama-bamai na Boko Haram ya yi ƙamari.
Sai dai ba kamar tasi da bas ɗin ba, shi a daidata sahu kan shiga cikin lunguna da kowane saƙo don ɗauka ko ajiye fasinja, wanda hakan kan taimaka wa waɗanda mazaunansu ke da nisa da bakin titi.












