Gwamnatin Kano ta samu umarnin kotu na rufe masallacin Sheikh Abduljabbar Kabara

Sheikh Abduljabar Kabara

Gwamnatin jihar Kano ta samu umarnin kotu na rufe masallacin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da kuma izinin hana shi wa'azin.

An samu umarnin ne daga Kotun Majistare ta Mohammed Jibrin, da ke Gidan Murtala, bayan da ofishin Kwamishinan Shari'a ya nemi hakan, kamar yadda takarda mai dauke da sa hannun ma'aiktar shari'ar da BBC ta gani.

A cikin takardar dai kotun ta bayar da umarni guda biyar kan mas'alar malamin kamar haka:

1. A rufe masallacin da makarantar Sheikh Abduljabbar da suke unguwar Filin Mushe ba tare da ɓata lokaci ba, har sai sakamakon binciken da ƴan sanda da hukumomin tsaro na jihar suka fitar.

2. Sheikh Abduljabbar ya dakatar da duk wani wa'azi ba tare da ɓata lokaci ba da duk wata magana da za ta jawo ruɗani a tsakanin al'ummar jihar Kano.

3. Dukkan kafafen yaɗa labarai su dakatar da yaɗa karatuttukan Sheikh Kabara har sai abin da sakamakon bincike ya fitar.

4. Dukkan hukumomi da cibiyoyin tsaro na jihar su tabbatar da cewa an bi waɗannan dokokin sau da ƙafa.

5. Dukkan hukumomi da cibiyoyin tsaro a jihar su ɗauki matakin da ya dace kan duk wani mai yin wa'azin da zai jawo rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummar jihar Kano.

Gwamnatin Ganduje 'ta yi wa Sheikh Abduljabbar Kabara daurin talala'

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano da ke Najeriya Sheikh Abduljabbar Kabara ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta yi masa daurin talala.

Gwamnati ta yi wa malamin daurin talala ne kwana guda bayan ta haramta masa yin wa'azi da tafsiri a fadin jihar.

Ana zarginsa da yin kalaman da ka iya tunzura jama'a a cikin wa'azin da yake gabatarwa.

Malamin ya tabbatar wa BBC Hausa rahoton da ke cewa an hana kowa shiga gidansa.

Ya shaida wa wakilinmu a Kano cewa: "Magana ta gaskiya ita ce wannan rahoto da ya zo maka gaskiya ne. Ina zaune a nan library (dakin karatu) sai ake cewa duk wanda ya zo zai shiga, wadanda suke mazauna gidan ana tare su a hana su shigowa, sai dai idan fita zai yi. Idan ya fita ba kuma ba zai dawo ba."

Ya kara da cewa ya yi mamakin daukar wannan mataki domin kuwa "mun dauka cewa karatu ne kawai ba sa so a yi. Ba mu san cewa har da shige da fice duk ba za a yi ba. Don haka ba mu tanaji abubuwan da za a bukata na rayuwa ba."

Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar ta Kano Abdullahi Umar Ganduje yake ganawa da malaman kungiyar izala, Kadiriyya da kuma Tijjaniya game da haramta wa malamin wa'azi.

Cikin wadanda suk halarci taron akwai malam Nura Manzo Arzai, Sheikh Sale Pakistan, Malam Bashir Alfurkan, Sheikh Matabuli, Shiekh Nasir Kabara, Malam Shehi Shehi mai Hula, Malam Abdulhadi Hotoro, da sauran su.

Mallam Nura Arzai ya nuna jin dadin sa tare sa goyon bayan gwamnati kan matakin da ta dauka na hana Sheikh Abduljabbar yin wa'zi da tafsiri.

A cewarsa hakan ya tabbatar da cewar Gwamna Ganduje ya amsa sunansa na Khadimul Islam, saboda yadda ya kawo karshen batanci da aka yi wa sahabban manzon Allah (SAW).

Sai dai Malam Abdulhadi Adam Hotoro ya ce ya kamata a ce a zartar da hukunci idan dai aka tabbatar da laifin da ake zargin Abduljabbar da yi wanda ya ce ya sabawa dokokin addinin Musulunci.

Wannan layi ne

'Gwamnatin jihar Kano ta zalunce ni'

Bayanan bidiyo, Bidiyon martanin Sheikh Abduljabbar Kabara kan hana shi wa'azi

Tun da farko Sheikh AbdulJabbar Sheikh Nasir Kabara ya bayyana dakatarwar da gwamanatin jihar Kano d ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".

Ya faɗa wa BBC cewa duk da ita gwamnati da kanta, ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar, ta tabbatar da abin da ake yi masa zalunci ne, amma ta dakatar da shi ba tare da ba shi damar kare kansa ba.

Shehin malamin ya ce taron da ya gudanar a makon da ya gabata na daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin, ganin cewar duk yunƙurin hana taron ya ci tura.

"Kwamishinan ilimi ya faɗa da yawun gwamnati cewa ana zaluntar Abduljabbar ne kuma abubuwan da malaman nan suke yi ba su da gaskiya ko kaɗan, sun shigar da siyasa ne cikin addini," in ji shehin malamin.

A cewarsa: "A matsayina na wanda ba kowan kowa ba, kamar kwamishinan ilimi ya ce ana zaluntar Abduljabbar, ai ya isa raddi ga gwamnati cewa abin da ta yi zalunci ne."

'Ba za mu bari mutum daya ya jawo mana rashin zaman lafiya ba'

A nasa bangaren, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sun dauki matakin ne domin hana tashin hankali a jihar.

Gwamna Ganduje ya shaida wa BBC Hausa cewa "ba za mu bari mutum daya ya jawo mana rashin zamna lafiya ba a wannan jiha tamu."

Ya ce a matsayinsa na gwamna yana goyon bayan duk wani mataki da jami'an tsaro za su dauka a kan malamin, ciki har da daurin talala, muddin za a samu zaman lafiya.

Ya musanta zargin da Sheik Abduljabbar ya yi cewa an sanya siyasa a cikin lamarin yana mai cewa shi malamain da kansa ne ya jawowa kansa matsala domin kuwa ya sha gaya wa magoya bayansa su yanka duk mutumin da ya je wurinsa domin ya kama shi.

Wannan layi ne