Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Idris Deby : Kotu ta ɗaure mutumin da ya ce shugaban Chadi ba shi da lafiya
Wata kotu a ƙasar Chadi ta ɗaure wani ɗan gwagwarmaya kare haƙƙin dan adam na ƙasar a gidan yari na tsawon shekaru uku da zummar gyaran hali.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta sa mu mutuman da laifin rubuta cewa shugaban ƙasar ba shi da lafiya kwarai da gaske, kuma ya na jinya a ƙasar Faransa .
An dai kama Baradine Berdei Targuio, shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasar a cikin watan Janairun shekarar 2020, bayan da ya wallafa labarin rashin lafiyar shugaba Idriss Déby a shafin shi na Facebook.
Kotun hukunta miyagun laifuka ta garin N'Djamena babban birnin ƙasar na Chadi ta bayyana laifin da aka same shi da aka aikatawa a matsayin 'keta doka tsarin mulki'
Wani ɗan adawar Mista Déby a siyasance, Saleh Kebzabo, ya ƙalubalaenci hukuncin da ya kira da rashin adalci mai kuma bita da ƙullin siyasa, tare da yin kira da a saki Baradine Berdei Targuio.
Yanayin da al'ummar kasar Chadi ke ciki
A daidai lokacin da ake tunkarar gudanar da zaɓen kasar, a cikin makon da ya gabata gwamnatin ƙasar Chadi ta sake sanar da haramcin gudanar da zanga-zanga ga masu adawa da gwamnati, sakamakon barazanar saɓa doka.
A dai cikin watan Afirlun gobe ne shugaban Déby zai sake tsayawa takarar neman shugabancin ƙasar a wa'adi na 6.
A cikin shekaru 30 da ya shafe a kan karagar mulkin ƙasar ta Chadi, ana zargin Déby da gudanar da mulkin kama- karya irin na kin-kari, baya ga zargin shi da gazawa wajen fuskantar matsalolin talauci da fatara da suka addabi mutane milyan 13 na kasar ta Chadi.
Duk da arziƙin man fetur da kasar ta Chadi take da ke da shi, ita ce ƙasa ta 187 daga cikin kasashe 189 da basu da bunƙasar rayuwar al'umma mai inganci, kamar yadda wanni rahoton hukumar majalisar ɗinkin duniya mai kulla da fanin ci gaban al'ummata ya sanar.
Ƙasar Chadi wadda ke yankin Afirka ta tsakiyar, ta yi iyakoki da kasashe kamar su Libiya da Nijar da Najeriya da Kamaru da Jumhuriyar tsakiyar Afirka da kuma kasar Sudan.