Uganda : Yadda sojoji suka lakaɗawa ƴan jarida duka

Majalisar Ɗinkin Duniya a Uganda ta la'anci harin da 'yan sanda da soji suka kaiwa' yan jaridar da ke aiko da rahotannin da suka shafi jagoran yan adawar ƙasar Bobi Wine.

Hakan ya faru ne yayin da yake mika koke ga Ofishin Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna irin cin zarafin da ake yi a kasar.

Hotunan bidiyo sun nuna mambobin jami'an tsaro suna bin 'yan jarida da duka da sanduna.

Jam'iyyar ƴan adawar Uganda ta ce da yawa daga cikin magoya bayanta sun bata bayan zaben da ya janyo rikici a watan jiya kuma sun yi zargin an azabtar da wasu.

Gwamnatin ta musanta hakan, amma ta ce ta kame mutane da dama saboda tayar da tarzoma da sauran ayyukan laifi.

Shugaba Yoweri Museveni ya kasance a kan mulki tun shekarar 1986, sannan ungiyoyin kare hakkin dan adam da dama a fadin duniya na zargin gwamnatinsa da take hakkin dan adam da kuma na yan adawa.

Zargin maguɗi a zaɓe

Shi dai Jagoran ƴan adawar Bobi Wine ya ce bai yarda da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi na baya bayan nan ba, kana yana fargabar halin da zai iya faɗawa tun bayan da sojoji suka kewaye gidansa.

Ya shaida wa BBC cewa ɗaruruwan sojoji sun tare a gidansa tare da iyalinsa, baya ga cin zarafin wasu magoya bayansa da suka riƙa yi.

Ranar Asabar ne hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen a hukumance, inda ta bayyana shugaba mai ci Yoweri Museveni a matsayin wanda ya samu nasara da tazara mai yawa.

Bobi Wine da sauran ƴan takara goma da suka shiga zaɓen sun yi zargin tafka maguɗi, da kuma hana wakilansu sanya ido.

Kwana biyu kafin zaɓen ne hukumomi suka katse hanyoyin sadarwa, wanda Bobi Wine ya ce ya taimaka wajen boye cuwa cuwar da aka tafka.