Shin ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Kudancin Najeriya za ta kawo karshen rikicin da ya barke?

Gwamnonin wasu jihohin Arewacin Najeriya na gudanar da wata ziyara a jihohin kudu maso yammacin kasar a kokarin wanzar da zaman lafiya bayan fadan da ya barke a tsakanin Hausawa da Yarbawa a makon jiya.

Gwamnonin jihohin Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Naija, Abubakar Sani Bello; Kebbi, Atiku Bagudu; da kuma Bello Matawalle na Zamfara, sun ziyarci takwaransu na jihar Oyo Seyi Makinde game da rikicin da ya faru tsakanin Yarbawa da Hausawa a Ibadan.

Kazalika gwamnonin za su gana da takwaransu na Ogun Dapo Abiodun idan anjima a yau, sakamakon hare-haren da ake zargin makiyaya sun kai a Yewaland lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane.

Wakilin BBC da ya je birnin na Ibadan ya ce ya kirga kaburbura 12 na mutanen da aka binne daga bangaren Hausawa, yana mai cewa al'umar Hausawa sun shaida masa cewa mutum 17 aka kashe daga bangarensu.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta ce mutum daya ne ya mutu sakamakon rikicin.

Lamarin ya faru ne bayan mutuwar wani Bayarabe a kasuwar Shasha sakamakon hatsaniyar da ta ɓarke tsakanin wani Bahaushe mai turin baro da wata Bayarabiya mai shago a kasuwar ranar Alhamis.

Rikicin ya kuma yi sanadin jikatar fiye da mutum dari da kuma kona shaguna da dama a kasuwar Shasha tare da raba daruruwan mutane daga gidajensu.

Ganau sun ce Bahaushen, wanda ke tura baron tumatur, ya faɗi a gaban shagon matar abin da ya sa tumaturin ya zube. Hakan ne ya sa matar ta ce dole ya tsince dukkan tumaturin, lamarin da ya kai ga rikicin da ya yi sanadin mutuwar wani Bayerabe.

Sake gina kasuwa

Kungiyar gwamnonin Nigeria ta ce za ta ba da gudunmuwa wajen sake gina kasuwar Shasha da aka kona a rikicin da aka yi tsakanin Yarabawa da Hausawa a karshen makon jiya.

Gwamnan jihar Kebbi wanda ya jagoranci tawagar gwamnonin arewa hudu zuwa jihar Oyo ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayani a fadar Sarkin Hausawan Shasha Malam Harun Mai Yasin.

Ya ce a yanzu haka sun kai wa mutanen da lamarin ya shafa gudunmuwa, sai dai bai yi karin bayani kan gudunmuwar ba.

Gwamnonin sun kuma kai ziyara fadar masaraucin gargajiyar Yarabawa na yankin Shasha Baale, da kasuwar Shasha.

Da yake jawabi, Sarkin Hausawa na kasar Ibadan, Alhaji Ahmed Dahiru Zangeru, ya bayyana cewa rikicin shugabancin kasuwar Shasha tsakanin Yarabawa da Hausa ne ya rura wutar tashin hankalin da aka fuskanta a karshen makon jiya.

'Labaran karya'

Wannan lamari dai ya sa wasu Hausawa da ke zaune a yakin na Yarbawa sun soma tattara kayayakinsu inda suke nufar yankunansu na asali da ke arewacin kasar.

Sai dai hakan ya sa masu ruwa da tsaki musamman gwamnoni suka tashi tsaye domin kwantar da hankulan al'ummominsu ciki har da ziyarar da suke yi haka a yankin kudu maso yammacin kasar.

Gabanin ziyarar tasu, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya shaida wa BBC cewa za su tabbatar 'yan arewacin Najeriya da ke zaune a kudancin kasar ba su fuskanci karin matsaloli ba, yana mai cewa "muna kira a gare su da su zauna lafiya."

Sai dai masana harkokin tsaro na ganin a yayin da ziyarar tasu take da alfanu sosai, ya kamata su yi amfani da irin wannan dama wajen ganin an yi adalci ga dukkan wanda aka zalunta a sanadin rikicin domin kare aukuwarsa nan gaba.

Wani masanin harkokin tsaro, Janar Ibrahim Sabo (mai ritaya), ya shaida wa BBC cewa: "Irin wannan ziyara tana da matukar amfani domin kuwa za ta bai wa gwamnonin damar sanin hakikanin abin da ya faru. Ka san idan fitina ta faru akwai masu watsa labaran karya. To, wannan zai sa su ga gaskiyar lamari sanna su san matakin da za su dauka domin warware matsalolin."

Ya kara da cewa su kansu 'yan asalin arewacin Najeriya da ke zaune a kudancin kasar za su samu kwarin gwiwa ganin cewa gwamnoninsu sun yi tafiyayya domin ganin abin da ya auku da kuma dauka mataki.

"Sai dai babban abin da ya kamata su mayar da hankali shi ne jaddada amfanin zaman lafiya da bin doka. Sannan su tabbatar an yi adalci ga dukkan wanda aka zalunta yadda hakan ba zai sake aukuwa ba," in ji shi.

Rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu ya sa wasu 'yan arewacin kasar da ke shafin Twitter sun kirkiri maudu'in #StopKillingNortherns domin jan hankulan duniya game da kisan da suka ce an yi wa 'yan Arewa wadada ba su ji ba ba su gani ba a yayin rikicin.