An kafa hukumar bincike kan harin majalisar dokokin Amurka

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga Amurka na cewa za a kafa wata hukuma ta musamman da za ta binciki harin da aka kai ginin majalisar dokokin kasar a farkon watan jiya.
Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi, ta ce hukumar da za a kafa za ta binciki ainihin abubuwan da su ka faru dangane da hatsaniyar ta 6 ga watan Janairu.
Wannan matakin ya biyo bayan wanke tsohon shugaba Donald Trump ne a shari'ar da aka yi ma sa bayan tsige shin da aka yi a karo na biyu saboda tuhumar da aka yi ma sa ta tunzura magoya bayansa da su hambarar da majalisar kasar.
A wata wasika da ta aika wa 'yan jam'iyyarta da Democrat mai mulkin kasar, Nancy Pelosi ta ce hukumar za ta kasance irin wadda aka kafa bayan hare-haren 12 ga watan Satumbar 2001.
Ta ce sabuwar hukumar za ta duba dalilan da su ka sa aka sami wadanda ta kira "Harin da 'yan ta'addan cikin gida su ka kai wa ginin majalisar dokokin Amurka."
Za ta kuma duba matakan da jami'ai su ka dauka gabanin kai harin, da kuma matakan da ma'aikatun gwamnatin kasar da 'yan sanda suka dauka bayan da harin ya auku.
Ana dai tuhumar fiye da mutum 200 da aikata laifuka daban-daban dangane da harin da aka kai wa majalisar dokokin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar.







