Ku San Malamanku tare da Sheik Ibrahim Ahmad Maqari

Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheik Ibrahim Ahmad Maqary a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon:

Fitacce malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheik Ibrahim Ahmad Maqri ya ce babban abin da ya sanya a gaba shi ne samar da makarantu ko zawiyyoyi ko masallatai wadanda za su dace da tsari na wannan karni.

Malamin, wanda shi ne kuma limamin babban masallacin Juma'a na Abuja, ya faɗi hakan ne a hirar da ya yi da BBC Hausa a shirinmu na musamman mai taken ''Ku San Malamanku''.

"Babu abin da na sanya a gaba illa kokarin yadda za mu samar da tsari na institution na addini. Idan an ce institution, ana nufin makarantu, ana nufin zawiyyoyi, ana nufin masallatai wadanda za su zama mu'assasat wadanda suka dace da zamanin da muke ciki, karni na ashirin da daya da kalubalen da ke cikin karni na ashirin da dayan, kuma su rika ba da gudunmawarsu a wannan tsari," in ji shi.

Ya kara da cewa muhimmin abu shi ne kada tsarin addini ya dogara da mutum daya.

Malamin ya ce ko da yake bai taba tsayawa ya kirga adadin littafan da yake rubutawa ba amma "za a iya cewa za su kai arba'in."

Ya ce akwai littafin da yake rubutawa yanzu wanda yake "kokarin dauko sababbin mas'aloli wadanda za su kara kyautata fahimtar matasa almajirai ilimi da addinin Musulunci gaba daya a zamanin da muke ciki wanda ke cike da tahaddiyat."

Wane ne Sheik Ahmad Maqry?

An haifi Sheik Ibrahim Ahmad Maqary a garin Zaria cikin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a shekarar 1976.

Sheikh ya bayyana cewa ya fara karatunsana firamare a garin Katsina bayan da aiki ya mayar da mahaifinsa can.

''Kakana wanda ya haifi mahaifina shi ya zo kasar Zaria daga garin Borno da niyyar neman ilmi, kuma bayan ya samu abin da yake so ya bukaci ya koma inda ya fito don ya cigaba da ilmantar da al'umma,'' in ji Sheik Maqary.

Ya kuma ce "amma sai sarki Zazzau na wancan lokacin ya ce ai shi malamai ba sa zuwa garinsa su bar garin, don haka sai ya ba shi gida ya ci gaba da zama yana ilmantarwa."

Malamin ya ce ya yi karatu gwargwado a gidan shahararren malami a garin Katsina Sheik Abba Abu.

Ya kuma ce malaman da ya zauna da su don daukar karatu a garin Zaria suna da dan dama, cikinsu akwai malam Tanimu Kusfa shahararren malamin fiqihu da sauran fannonin ilimi.

Sannan akwai babban malami a Zaria Malam Bala Kusfa a wannan lokacin "kanin mahaifina yana daga cikin almajiransa, don haka yana daukarsa yana kai shi zaurensa don sauraron karatun."

Kafin tafiyarsa kasar Masar karo karatu, Sheik Maqary ya hadu da daya daga cikin malaman da suka fi yin tasiri a rayuwa, Sheik Muhammadu Amin Abdullahi mutumin Okene.

Malamin ya ce a kasar Masar babban guzirin da zai iya cewa ya samu shi ne haduwarsa da babban malaminsa, abin alfaharinsa a dukkan fannonin karatu da rayuwarsa Sheik Ibrahim Saleh al- Hussaini, kuma shugaban babbar majalisar Fatwa ta Najeriya.

Ya je kasar Masar karatu a daidai lokacin da ya bude makaranta

Yawanci malamansa ba 'yan Najeriya ba ne, sun zo daga kasashen Mauritania da Morocco, don haka ya yi amfani da wannan damar wajen daukar wasu fannoni daga cikin ilmi daga hannun malaman.

Haddar Al Kur'ani mai girma

Malamin ya ce yana da kimanin shekara 13 har zuwa 14 ya yi haddar AlKur'ani mai girma a makarantar da aka bude mai suna Madarasatul Faidatul Islamiyya ta gidan Sheik Yahuza Zaria.

A wannan lokacin ne ya samu babban sauyi a rayuwarsa, bayan da mahaifinsa ya cire shi daga tsarin karatun boko bayan ya kammala makarantar sakandare ya mayar da shi makarantar da yake jagoranta da ake kira Jama'atu 'College of Arabic and Islamic Studies' kuma a lokacin ne ya muhimmantar da harshen Larabci musamman ilmin ginin ka'idar jimla da ake cewa ilmim nahawu.

"Lallai mun yi karatu mai yawa a wannan lokacin, mun haddace mafi yawan litattafan da ake karantawa a wannan lokacin," in ji shi.

Malamin ya kuma ce yana da wani yanayi da ba ya iya barci da dare da sauki, inda a lokuta da dama mahifinsa idan ya ga ya ki tashi ya daina karatu don ya je ya kwanta sai ya kashe duka wutar gidan.

Sheik Maqary Farfesa ne da ya koyar da Larabci a Jami'ar Bayero da ke Kano amma ya ritaya a 2020.

Wasu karin labaran da zaku so karantawa