Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana hanyoyin magance matsalar fyaɗe a Najeriya

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa, ya bayyana matakan da suka kamata a dauka domin shawo kan matsalar fyade da ta addabi kasar.

A tattaunawarsa da BBC, Sheikh Daurawa, ya jero matakan da suka kamata bi wajen magance wannan matsala, ciki har da haramta wa duk wanda aka samu da laifin fyade rike duk wani mukami na gwamnati.

Ya kara da cewa akwai bukatar "ilimantar da mutane da wayar da kansu. A duba a ga me yake kawo fyaden nan? Su wa ake yi wa? Meye dalilin da ake yin fyaden nan? Sannan kuma wacce hanya za a bi a dakile fyaden nan?".

Latsa bidiyon da ke sama domin kallon karin bayanin Sheikh Daurawa kan wanna batu: