Kalubalen da ke gaban sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na nada sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar bayan ya kori hafsohin da 'yan kasar suka dade suna korafi a kansu, wani sabon babi ne aka bude kan yadda ake tunkarar rashin tsaron da ke addabar Najeriya.

Shugaba Buhari ya nada sabbin manyan hafsoshin sojin kamar haka: Janar Leo Irabor, babban hafsan tsaro; Janar I. Attahiru - babban hafsan sojan ƙasa; Rear Admiral A.Z Gambo - babban hafsan sojan ruwa; da kuma Air-Vice Marshal I.O Amao - babban hafsan sojan sama.

Sun maye gurbin Janar Abayomi Olonisakin, Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar wadanda ya nada a 2015 bayan ya lashe zabe a karon farko.

Shugaba Buhari bai bayyana dalilin cire su ba.

Sai dai ya sauke su ne lokacin da 'yan kasar suka cire rai bayan sun dade suna kiraye-kirayen a ture musu rawani sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar.

Nadin sabbin manyan hafsoshin tsaron na faruwa ne a yayin da kasar ke fuskantar karin matsalolin tsaro kan wadanda suka taras lokacin da suka soma aiki.

Kalubalen tsaro na 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da hare-haren Boko Haram a arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya.

Kazalika akwai matsalar da ta kunno kai a kudu maso yamma ta makiyaya da kuma tawayen masu fafutukar ballewa daga Najeriya da ke kudu maso gabashin kasar, na cikin manyan batutuwan da ke fuskantar sabbin manyan hafsoshin tsaron.

Hare-haren 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane

Masu nazari kan harkokin tsaro na ganin matsalar farko da za ta soma kallon sabbin manyan hafsoshin tsaron ita ce ta 'yan fashin daji da barayin mutane domin karbar kudin fansa wadda ta gallabi arewa maso yammacin kasar.

Wannan matsala ta yi karami ne a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari inda aka yi garkuwa daruruwan mutane yayin da aka kashe da dama.

Wani abu da ya kara fito da matsalar ga idon duniya shi ne yadda a watan Disambar 2020 'yan bindiga suka hari makarantar sakandaren kwana ta maza da ke garin Kankara na jihar Katsina, inda suka sace dalibai fiye da 300.

Kodayake an sako su daga baya, amma al'ummar irin wadannan yankuna da ke jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna, na ci gaba da bacci da idanu daya saboda tsoron masu satar jama'a.

Rikicin Boko Haram

Duk da yake masana harkokin tsaro na ganin sojin Najeriya sun samu galaba mai yawa a kan mayakan kungiyar Boko Haram a shekarun baya bayan nan, amma suna ganin akwai jan aiki wajen kawar da kungiyar ganin yadda har yanzu take iya kai hari ciki har da a sansanonin soji.

Hasalima yankan ragon da mayakan kungiyar suka yi wa mutum fie da 30 a garin Zabarmari na jihar Borno a shekarar da ta gabata, ya nuna cewa har yanzu kungiyar tana da karfi.

Kazalika sabbin manyan hafsoshin za su so kama shugaban wani bangaren na kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau, wanda sau da dama ana bayar da sanarwar kashe shi amma daga bisani ya musanta hakan.

Sauran matsalolin tsaro

Haka kuma wadannan sabbin hafsoshin tsaro za su yi fama da masalolin da ke faruwa a kudu maso gabashi na kungiyar IPOB da ke son ballewa daga Najeriya.

Kazalika akwai matsalolin makiyaya a kudu maso yamma inda ko a makon na sai da aka yi sulhu tsakanin al'ummomin yankin da makiyaya wadanda ake zargi da satar mutane da aikata wasu laifuka, zargin da suka musanta.

Wani batu kuma shi ne na 'yan fashin teku da ke gabar tekunan Najeriya wadanda, kodayake sun yi sauki idan aka kwatanta da sekarun baya, amma har yanzu ana jin amonsu.

Karfafa gwiwar sojoji da ke fagen fama

Masana harkokin tsaro irin su Barrista Audu Bulama Bukarti sun ce kodayake ba lallai ne abubuwa su sauya da wuri ba amma nadin sabbin hafsoshin tsaron zai karfafa gwiwar 'yan Najeriya ciki har da 'yan majalisar dokoki wadanda suka kwashe tsawon lokaci suna kira a sauke tsoffin hafsoshin saboda gazawarsu.

A cewarsa: "Ya kamata wadannan sabbin manyan hafsoshin tsaro su saurari mutanen da ke kan iyakokin Najeriya inda ake wajen shigowa kasar. Sannan ya kamata su karfafa gwiwar sojoji da ke fagen fama ta hanyar ba su kayan aiki masu karko da alawus-alawus da sauransu."

A nasa bangaren, Malam Kabiru Adamu, masani kan lamuran tsaro a Najeriya da kuma yankin Sahel, ya shaida wa BBC Hausa cewa mutanen da aka naɗa sabbin jini ne da za su karɓi aiki da ƙwarin guiwar ganin sun samu nasara.

Hafsoshin da aka kora da wadanda aka nada

  • Babban hafsan tsaro: Manjo Janar Leo Irabor ya maye gurbin Jnar Abayomi Olonisakin
  • Sojin Kasa: Majojo Janar I Attahiru ya karbi aikin Laftanar Janar Tukur Buratai
  • Sojin Ruwa: Rear Admiral A Z Gambo ya gaji Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas
  • Sojin Sama: Air-Vice Marshal I O Amao ya maye gurbin Air Marshal Sadique Abubakar