Donald Trump: Shugaban Amurka na 45 ya yi bankwana da 'yan kasar

Donald Trump on board Air Force One (file pic)

Asalin hoton, Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabinsa na bankwana, wanda a ciki yake cewa: "Mun yi abin da ya kawo mu - har ma da kari."

A wani sakon bidiyo da aka wallafa a YouTube, shugaban ya ce ya "sauke nauyin da aka dora mana, wanda shi ne dalilin da ya sa kuka zabe ni."

Sai dai har yanzu Mista Trump bai amince da shan kaye a zaben watan Nuwamba ba, zaben da Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya lashe

Za a rantsar da Joe Biden matsayin shugaban Amurka na 46 ranar Laraba.

Makonni biyu na karshen mulkin Mista Trump sun kasasnce cike da takaddama bayan wani hari da mabiyansa suka kai ginin majalisar dokokin kasar, inda suka ce suna son sauya sakamakon zaben shugaban kasar saboda gwaninsu ya sha kaye.

"Hari irin wannan yana da mummunan tasiri kan dukkan abubuwan da mu Amurkawa ke alfahari da shi ne. Ba za a taba amincewa da shi ba," in ji Trump.

Sai dai bai ambaci sunan wanda zai gaje shi ba, duk da cewa ya nuna karshen mulkinsa ya zo.

"Mun dauko aikin mayar da martabar Amurka ga dukkan Amurkawa. Yayin da nake kammala wa'adina a matsayin shugaban Amurka na 45, ga ni tsaye gare ku ina alfahari da abubuwan da muka cimma tare."

Ya kara da cewa: "Mun cimma dukkan abubuwan da muka sa a gaba har ma da wasu na daban."

"Yayin da kuma a wannan makon za mu kaddamar da sabuwar gwamnati, muna son a yi ma ta addu'a domin Amurka ta kasance cikin zaman lafiya da karuwar arziki. Muna kuma mika fatan mu na alheri a gare su," a cewar Mista Trump.

Ya kuma soki masu amfani da tashin hankali wajen cimma muradai na siyasa.

A cewarsa: "Dukkan Amurkawa ba su ji dadin harin da aka kai wa ginin majalisar kasarmu ba."

Ya kuma ce rike mukamin shugaban Amurka abin alfahari ne da ba ya misaltuwa.

"Ina mika godiya ta ga wannan abin alfaharin, wanda haka na dauke shi, babban abin alfahari," a cewarsa.

Ya bukaci da kada su manta cewa duk da cewa a "matsayinmu na Amurkawa, za mu rika samun bambance-bambance, amma kasarmu kasa ce ta mutane masu kwazo da mutunci da biyayya da kuma masu son zaman lafiya, wadanda ke son kasarmu ta bunkasa, ta kuma zama mai nasarori. Lallai mun kasance kasa abar alfahari."

Trump ya yi afuwa ga mutane da dama

Steve Bannon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Steve Bannon ya musanta aikata laifi

A yayin da shugaban Amurka yake bankwana da mulki a ranar Laraba, ya sanar da yin afuwa ga mutum fiye da 73 ciki har da tsohon mai ba shi shawara Steve Bannon.

An tuhumi Mista Bannon da almundahana da kudin da aka ware domin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico.

Kazalika Mista Trump ya yi afuwa ga mawaka Lil Wayne da Kodak Black da kuma tsohon Magajin birnin Detroit Mayor Kwame Kilpatrick da sauransu.

Tun da farko shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Mitch McConnell ya yi wa Mista Trump wata kakkausar suka, inda ya dora masa alhakin harin da magoya bayansa suka kai kan majalisar Amurka mako biyu da suka gabata.

Mista McConell ya kuma ce 'yan bangar sun sami karfin gwuiwa ne bayan da shugaban ya tunzura su kuma ya rika cika su da karairayi.

Mista Trump na fuskantar wata shari'a a majalisar dattawa kan rawar da ya taka bayan tsige shin da majalisar wakilai ta yi.