Kamfanin Boeing zai biya tarar biliyan $2.5 kan haɗuran jiragen 737 Max

Kamfanin kera jiragen sama na Boeing, ya amince da biyan tarar dala biliyan biyu da rabi $2.5bn na tuhumar da aka yi masa kan aikata babban laifin cewa ya boye wasu bayanai ga jami'an lura da kare haddura game da jiragensa samfurin 737 Max.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce kamfanin ya zabi ''samun riba a kan nuna gaskiya'', tare da hana a gano matsalolin da ke tare da jiragen, wadanda suka yi munanan hadurra.

Kusan dala miliyan dari biyar ce ($500m) za a bai wa iyalan mutum 346 da suka mutu a hadarin jiragen.

Boeing din ya ce kudirin yarjejeniyar ya nuna yadda kamfanin ''ya fadi-ba-nauyi''.

Jagoran kamfanin na Boeing, David Calhoun ya ce: "Na tsananin yadda cewa shiga wannan yarjejeniya abin da ya kamata mu yi ne - matakin da ya nuna a fili cewa fatan da mutane ke da shi a kanmu da kimarmu sun fadi kasa warwas.

"Kudirin wannan yarjejeniya wata gagarumar tunatarwa ce ga dukkanmu kan yadda nauyin da ya rataya a wuyanmu na nuna gaskiya ga hukumomi ke da muhimmanci, sannan da irin mummunan sakamakon da zai biyo baya wa kamfaninmu muddin dayanmu ya gaza cimma irin fatan da ake da shi a kanmu.''

'Halin zamba da yaudara'

Ma'aikatar shari'a ta Amurka, ta ce jami'an kamfanin na Boeing sun boye bayanai game da sauye-sauyen da aka yi wa na'ura mai sarrafa tukin jirgin da kanta, da aka fi sani da MCAS, wanda bincike suka danganta irinsa da na hadurran jirage a kasashen Indonesia da Ethiopia a shekarar 2018 da 2019.

Matakin ya nuna cewar babu wasu bayanai game da na'urar a kundi mai dauke da horaswa a rubuce ga matukin jirgin sama, wacce ta rika nuna wa matukin jirgin bayanai masu kuskure, ta tilasta wa jirgin subutowa kasa jim kadan bayan tashinsa.

Kamfanin Boeing din ya shafe watanni shida bai bayar da hadin kai wajen gudanar da binciken ba, in ji ma'aikatar shari'ar.

"Munanan hadurran jiragen ''Lion Air 610'' da ''Ethiopian Airlines 302'' sun bankado halayyar zamba da yaudara daga ma'aikatan daya daga cikin kamfanonin kera jiragen saman a jigila mafi girma a duniya," in ji mataimakin babban lauyan Amurka David Burns.

"Ma'aikatan kamfanin Boeing sun zabi hanyar samun riba a maimakon a kan fadin gaskiya, ta hanyar boye wa hukumomin lura da zirga-zirgar jiragen sama FAA bayanai game da ayyukan jirginsu kirar 737 Max, suka rika kokarin boye duk wasu kafofi da za sun nuna irin yaudararsu.''

Karkashin tsarin yarjejeniyar, an tuhumi kamafanin na Boeing da laifi daya na kitsa makarkashiyar zambatar Amurka, da za a janye bayan shekara uku idan kamfanin ya ci gaba da bin ka'idar da yarjejeniyar ta shimfida.

Kamfanin ya kuma amince ya biya tarar dala biliyan dubu dari biyu da arba'in da uku da miliyan dari shida ($243.6m).

Amma kuma lauyoyin wadanda hadarin jirgin kamfanin Ethiopian Airlines ya rutsa da su, sun ce yarjejeniyar ta ranar Alhamis ba za ta kawo karshen karar da suka shigar kan kamfanin na Boeing ba.

"Zarge-zargen da suka bayyana a cikin yarjejeniyar tuhumar tamkar farawa ne, kan aikata ba daidai ba da kamfanin na Boeing ya yi — kamfanin da zai biya biliyoyin daloli don kauce wa daukar nauyin aikata babban laifi, yayin da yake jan kafa da kuma kalubalantar iyalan a kotu,'' in ji wata sanarwa daga lauyoyin da ke wakiltarsu.

Sun kuma kara da cewa bai kamatar a ce hukumar ta FAA "ta amince wa jirgin na 737 Max sake ci gaba da aiki ba, har sai an shawo kan matsalolin jirgin sosai, sannan an yi masa garanbawul na kare rayuka''.

Boeing ya ce ya riga ya shawo kan matsalolin da ke tattare da jirgin na Max, yayin da ya koma bakin aiki a Amurka cikin watan Disamba.

'Ba lallai bane a sa-idon ya tsaya a nan'

Sharhi daga Theo Leggett ( wakilin BBC kan harkokin kasuwanci)

A halin da ake ciki, za ka iya cewa kamfanin ya dauki lamarin da wasa.

Ya kauce wa gurfana a gaban kotun, da kuma babban bangare da ya shafi biyan diyya ga kamfanonin jiragen saman - adadin da ya dace wanda me yiwuwa daga karshe za su biya.

Kamfanin ba tare da wata-wata ba na son ya yi amfani da wannan dama wajen shata layi kan daya daga cikin abubuwa masu tsauri da ya taba fuskanta a cikin tarihinsa.

A yayin da jirgin na 737 Max ya koma yin zirga-zirga, ba lallai bane sa-idon da ake yi kan kamfanin Boeing da hukumar ta FAA ya tsaya a nan.

Masu sukar da suka hada da iyalan wadanda hadurran suka rutsa da su, da lauyoyi, da 'yan siyasa na ci gaba da jajircewa a kan dasa ayoyin tambaya game da jirgin - kuma suna ci gaba da neman amsoshi.