737 Max: An amince wa Boeing dawowa sararin samaniyar Turai

Hukumar da ke lura da lafiyar jiragen sama ta Turai ta fadawa BBC cewa ta tabbatar da lafiyar jirgin Boeing samfurin 737 Max.

An dakatar da 737 Max a watan Maris ɗin bara, bayan da yayi hadari har sau biyu da hakan yayai sanadin salwantar rayuka 346.

Dama Amurka da Brazil sun amince masa da ya dawo da aiki sararin samaniyarsu.

A yanzu itama hukumar ta EASA da ke kula da sufurin jiragen sama a Turai ta tabbatar da cewa jirgin ba shi da wata matsala, kuma ta aminta ya dawo bakin aiki a fadin nahiyar a tsakiyar watan Janairu.

Hadarin 737 Max na farko ya faru ne a watan Oktoban 2018, a lokacin da jirgin mallakar Lion Air ya faɗa a wani teku da ke kusa da Indonesia.

Kuma watanni huɗu bayan haka ne samfurin jirgin mallakar Ethiopian Airlines ya faɗi jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama da ke Adis Ababa.

A duka haɗurran biyu, masu bincike sun ta'allaƙa faruwarsu ne da matsalar wata na'ura da ke kunna kanta da ke sa jirgin ya rikito ƙasa da kansa.

A cewar shugaban hukumar EASA Patrick Ky, ba matsalar da ta haddasa faduwar 737 Max har sau biyu ce kaɗai suka duba ba, sun yi wa jirgin binciken ƙwaƙwaf kuma sun tabbatar da lafiyarsa a wannan karon.

Hukumar ta kuma shata cewa dole ne matuƙan jirgin su halarci wani horo na musamman, tare da yin 'tuƙn gwaji' ga duka jiragen Boeing samfurin 737 Max.