Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Tigray: Habasha za ta gyara Masallacin Najashi da 'Sahabban Annabi' suka gina
Gwamnatin Habasha ta yi alkawarin gyara wani masallaci da ya shafe daruruwan shekaru, wanda aka rusa a rikicin watan jiya a yankin Tigray.
Rahotanni sun ce an harba wa Masallacin Najashi bom. An lalata hasumiyar masallacin da kuma kaburburan wasu jagororin Musulunci.
Gwamnati ta ce za ta kuma ta gyara wata coci mai makwaftaka da masallacin, wacce ita ma aka lalata.
Mazauna yankin sun yi amanna cewa sahabban Manzon Allah SAW da suka yi hijira zuwa Habasha su ne suka gina masallacin.
Sun gujewa cuzgunawa ne da cin zarafin da mutanen Makka suke yi musu a lokacin, kuma Najashi ya ba su mafaka a masarautar Aksum a lokacin.
Mazauna yankin sun yi amanna cewa awai kaburburan sahabbai 15 a wurin da aka lalata.
Sun kuma yi imani da cewa masallacin ne mafi tsufa a Afirka, sai dai wasu sun ce wani masallaci a Masar ya fi shi daɗewa.
Masallacin yana kusa da garin Wukro, mai nisan kilo mita 800 daga babban birnin kasar, Addis Ababa.
An kuma rusa wata Cocin Kiristocin gargajiya masu bin ra'ayin 'yan mazan jiya, sai dai babu karin bayani.
Wata hukuma a Turkiya ta kaddamar da wani aiki a 2015 na gyaran masallacin, tana cewa tana so ta adana tarihin masallacin sannan tana so ya zama wajen da masu yawon bude ido na addini za su ringa ziyarta.
Masallacin da kuma wata coci da ke kusa da shi an lalata su ne yayin rikicin da aka shafe wata guda ana yi wanda ya janyo aka tumbuke jami'iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF) daga mulki a yankin ranar 28 ga watan Nuwamba.
Me ya faru da masallacin?
Wata kungiya mai zaman kanta a Belgium, Europe External Programme with Africa, ta ba da rahoton cewa an rusa Masallacin na Najashi da farko ranar 18 ga watan Disamba sannan sojojin Habasha da na Eritriya suka wawashe kayan cikin masallacin.
"Majiyoyin Tigranya sun ce mutane sun mutu yayin da suke kokarin kare masallacin," a cewar kungiyar.
Gwamanati ba ta ce komai ba kan rahoton. Gwamnatocin Etitriya da na Habasha sun musanta cewa sojojin Eritriya sun shiga yankin Tigray don taimakawa a yakin da aka yi da TPLF.
A ranar Litinin, gidan talabijin din Haabasha ya ambato mazauna yankin na cewa dakarun TPLF sun haka ramuka a kewayen masallacin, sai dai ba su ba da karin bayani ba.
Gwamnati ta sanyawa kafofin wasta labarai tsattsauran takunkumi a yankin na Tigray, abinda ya sa zai yi wuya a gano ainihin abinda ke fruwa. An kuma hana kungiyoyin agaji shiga yankin.
A wata hira da sashin BBC Amharic, mataimakin darakta na Hukumar Adana Tarihi ta Habasha, Abebaw Ayalew yace za a tura tawaga don duba irin barnar da aka yi wa masallacin da cocin kafin a gyara su.
"Wadannan wuraren ba wai kawai wuraren ibada ba ne, wuraren tarihi ne ga duka kasar Habasha," a cewarsa
Wane irin muni rikicin ya yi?
Babu cikakken mutum nawa aka kashe a rikicin, sai dai a baya Shugaban Habasha Mista Abiy yace sojoji ba su kashe farar huka ko daya ba lokacin yakin da ya kai ga tumbuke TPLF daga mulki.
Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi kira a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen da duka bangarorin ke wa juna, ciki har da yi wa fararen hula kisan kiyasahi da harbe-hare da sace-sace a yankukuna fararen hula da asibiti.
Fiye da mutum 50,000 sun tsallaka Sudan don gujewa rikicin.
Menene dalilin yaƙin?
Yakin ya barke ne a farkon watan Nuwamba, yayin da Firaminista Abiy Ahmed ordered ya bai wa sojoji umarni su kaddamar da hare-hare kan dakarun yankin Tigray.
Ya ce ya yi hakan ne a matsayin martani kan wani hari da aka kai wa wani sansanin sojoji da dakarun gwamnatin ke ciki a Tigray.
Rikicin ya zo ne bayan watanni da samun sabani tsakani gwamnatin Abiy da shugaban TPLF - jam'iyyar da ta mamaye yankin.
Jam'iyyar ta shafe kusan shekara 30 ana damawa da ita a gwamnatin kasar, kafin Mista Abiy ya jinge ta bayan ya hau mulki a 2018, yayin da ake tsaka da zanga-zanagr kin jinin gwamnati.
Abubuwa biyar dangane da Tigray:
1. Masarautar Aksum was na da cibiya a yankin
An bayyana ta cikin daya daga manayan masu ci gaba shekaru dubbai da suka gabata, ta taba zama masarauta mafi karfi tsakanin daulolin Rum da Fasha.
2. Wuraren da suka rage na birnin Aksum wuraren tarihi ne na Majalisar Dinkin Duniya.
Wuraren da aka gina tsakanin karni na daya da na 13, na kunshe da gine-gine na mutan da, da fadoji na sarauta, da kaburburan sarakai da coci wacce wasu suka yi amanna cewa a nan aka ajiye Akwatun Alkawari (The Ark of the Covenant).
3. Mafi yawan mutane a yankin Tigray Mabiya Kiristancin gargajiya ne
Asalin kiristocin yankin ya kai shekara 1,600.
4. Babban harshen mutanen yankin shi ne Tigrinya
Daya daga manyan harsuna da akalla mutum miliyan bakwai ke magana da shi a fadin duniya
5. Ridi shi ne babban abinda ke kawo musu kudi
Ana kai shi Amurka da sauran kasashe.