Kullen korona a Birtaniya: Sabbin dokokin zaman gida da aka saka

Ya zama dole mutane a duka fadin Ingila da yankin Scotland su zauna a gida, baya ga wasu mutane kalilan da suka samu izini saboda wasu dalilai, yayin da sabbin dokokin kullen korona suka fara aiki a yankunan biyu.

An rufe makarantu ga akasarin dalibai a yankunan Ingila, da Scotland da Wales, yayin da a Ireland ta Arewa za a su samu ''karin wa'adi na yin karatu daga gida''.

Ana sa ran dokokin Ingila za su kasance har zuwa tsakiyar watan Fabrairu, yayin da yankin Scotland za su sabunta nasu a karashen watan Janairu.

Firaiminista Boris Johnson ya yi gargadin cewa makonni masu zuwa za su kasance ''mafiya tsauri''.

Hakan na zuwa bayan da Birtaniya ta shaida karin yaduwar cutar korona 58,784 a ranar Litinin, baya ga mutuwar mutane 407 a cikin kwanaki 28 da yin gwajin kwayar cutar.

Bayan da ya sanar da kullen koronar a Ingila, Mista Johnson ya ce asibitoci ''sun kara fuskantar kalubale sakamakon cutar ta korona fiye da ko wane lokaci, tun bayan barkewar annobar''.

Ya umarci sauran jama'a da su kasance a cikin gidajensu, banda wasu kalilan - kamar masu ayyuka na musamman da suka jibanci bukatu na kiwon lafiya, da sayen kayan abinci, motsa jiki da sauran ayyuka da ba zai yiwu a gudanar da su a cikin gida ba - sannan ya ce makarantu da kwalejoji su koma yin karatu daga nesa wato daukar darussa daga gida ga akasarin dalibai.

Ya kuma kara da cewa, duka tsofaffin da ake kula da su a cibiyoyi daban-daban da masu kula da su, da duk wanda ya kai shekara 70 zuwa sama, da ma'aikatan kiwon lafiya da masu aikin al'umma, da wadanda ke da wani zaunannen ciwo, za a yi musu allurar riga-kafin korona a tsakiyar watan Fabrairu.

Duk da cewa ka'idojin za su fara zama doka da sanyin safiyar ranar Laraba, Firaiministan ya ce yanzu haka mutane sun fara bi.

A ranar Litinin ne, Babbar Minista Nicola Sturgeon ya fitar da dokar zaman gida ga yankin Scotland, da ta fara da tsakar dare har ya zuwa karshen watan Janairu.

A kullen koronar na yankin Scotland, wanda ya shafi kewaye da kuma yammacin gabar tsibirin Skye, ya kuma hada da rufe makarantu da wuraren ibada da kuma haramta wasan motsa jiki na mutane da yawa.

"Ba wai ina cika baki bane da na ce na fi damuwa da halin da muke ciki a yanzu, fiye da yadda na damu a ko wane lokaci tun a cikin watan Maris na shekarar da ta wuce,'' in ji Ms Sturgeon.

A yankin Wales, inda aka shiga cikin kullen korona tun daga ranar 20 ga watan Disamba, makarantu da kwalejoji za su kasance a rufe har ya zuwa 18 ga wata Janairu.

Ku karanta sabbin dokokin na Ingila

Mutane ba za su fita daga gidajensu ba in dai ba da wasu dalilai na musamman ba, kamar yadda ya faru a kullen farko a cikin watan Mayun shekarar data wuce.

• Wannan ya hada da muhimman bukatu na kiwon lafiya, da sayayyar kayan abinci, da motsa jiki da aikin da ba zai yiwu a gudanar daga cikin gida ba.

• Za a rufe duka makarantu da kwalejoji ga akasarin dalibai daga ranar Talata tare da daukar darussa daga gida har ya zuwa cikin watan Fabrairu.

• Ba za a gudanar da jarrabawar karashen shekara ba lokacin wannan bazarar kamar yadda aka saba.

• Kada daliban jami'a su dawo harabar makaranta kuma za su rika karbar darussa ta yanar intanet.

• Gidajen cin abinci za su ci gaba da kai abincin ga masu saye daga gida, amma an haramta kai barasa.

• Dole a rufe wuraren motsa jiki da wasanni na waje - kamar filayen wasanni, da filayen wasannin golf da na kwallon tennis da na motsa jiki.

• Amma wuraren wasannin yara na wajen za su ci gaba da kasancewa a bude.

• Ba a amince da wasannin kwallo ko motsa jiki na ganin dama ba, amma za a ci gaba da gudanar da manyan wasanni kamar na gasar wasan kwallo irin su Premier League.

Cikin kwaryar yankin Scotland yammacin gabar tsibirin Skye:

• Makarantun naziri, da firamare, da na sakandare - za su ci gaba da kasancewa a rufe ga akasarin dalibai har ya zuwa cikin watan Fabrairu. Za a koma daukar darussa ta yanar intanet.

• Mutune za su fita daga gidansu saboda dalilai na muhimman bukatu kawai, kamar yadda ya faru a kullen farko na watan Maris din shekarar bara.

• Adadin mutane biyu ne daga akalla gidajen iyalai biyu za su iya haduwa a waje, amma ban da kananan yara kasa da shekara 11 da za su iya wasanni a tare a waje.

• Wuraren ibada za su kasance a rufe, in baya ga gudanar da bukukuwa a ciki (mutum biyar kacal) da jana'iza (mutane 20 kacal). An haramta kwanan addu'a ga mamaci.

• Za a tsaurara kan batun muhimman shaguna da ke da harabobi kamar su - wuraren wasan zamiyar kankara, manyan shaugunan sayar da kaya, da wuraren sayar da kayan kwalliya da aka bukaci su kasance a rufe.