Saudiyya ta sasanta da maƙwabciyarta Qatar

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin ƙasashen yankin Tekun Fasha sun rattaba hannu kan wani daftari yayin wani taron ƙoli a Saudiyya da nufin kawo karshen rikicin difilomasiyya tsakanin ƙasashen da kuma Qatar.
Lokacin da suka isa wurin taron Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad al-Thani da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, sun rungumi juna a wani mataki na sasantawa.
Wannan ne karon farko da Sheikh Tamim ya halarci taron tun bayan da Saudiyya da Daular Larabawa da Bahrain suka ƙaƙaba wa ƙasarsa takunkumi kan zarge-zargen goyon bayan 'yan ta'adda.
'Yar ƙaramar ƙasar mai arzikin man fetur ta musanta zargin sannan ta yi watsi da jerin sharuɗɗan da maƙwabtan nata suka gindaya mata, ciki har da katse hulɗa da Iran da kuma gidan talabijin na Aljazeera da take gudanarwa.
Nan gaba za a sanya hannu kan yarjejeniya ta ƙarshe wadda da za ta warware taƙaddamar baki ɗaya.

Wakilin BBC Frank Gardner ya duba takaddamar da ta janyo rarrabuwar kawuna tsakanin makwabtan biyu - Saudiyya da Qatar.
An shafe watanni ana tattaunawa kafin aka cimma yarjejeniyar dage wannan takunkumin, wanda yawanci kasar Kuwait ce ta jagoranci tuntubar junan da aka yi, amma Amurka ma ta taka muhimmiyar rawa a lokacin da mulki shugaba Trump ke kawo wa karshe.
Hanin da Saudiyyar da wasu kasashen suka kakaba wa Qatar ya yi ma tattalin arzikinta illa, har ma da ikirarin hadin kai da kasashen yankin Gulf suka dade suna yi. 'yan Qatar ba za su yi saurin matawa da abin da suke kallo a matsayin cin amana daga makwabtan nasu na yankin na Gulf ba.
Amma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayyana shakku cewa da wuya Qatar ta sauya halayenta.
Duk da cewa Qatar ta musanta goyon bayan ayyukan ta'addanci, amma ta dade tana ba kungiyoyin siyasa da ke Gaza da Libya da wasu wurare tallafi, musamman ma kungiyar nan ta 'Yan uwa Musulmi da Hadaddiyar Daular Larabawa ke kallo a matsayin barazana ga tsarin siyasar kasar na sarautar gargajiya.
A wani fagen kuma, takunkumin da Saudiyyar ta kakaba wa Qatar ya kara hada kan kasar da abokan gaban Saudiyyar biyu: Turkiyya da Iran.

Ta ya aka kula wannan yarjejeniyar?
Ministan harkokin waje na Kuwait Ahmad Nasser al-Sabah ne ya sanar da sabunta dangantakar a talabijin.
Gwamnatin Amurka ta shiga tsakani kuma ta taka rawa mai muhimmanci inda har surukin shugaban Amurkan Jared Kushner wanda shi ne babban mai ba shgaban shawara kan harkokin Gabas ta Tsakiya zai halarci bikin sanya hannun ranar Talata.
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al Thani ya amince da goron gayyatar da Sarki Salama na Saudiyya ya mika ma sa kuma zai halarci taron kolin da kansa.
Wata majiya ta ce bude kan iyakokin Saudiyya da Qatar da Saudiyyar ta yi na cikin abubuwan da aka tsara domin ba Sarkin na Qatar karfin gwuiwar halartar taron.
A shekarar 2017, yayin da aka fara kakaba wa Qatar jerin takunkumin, Sarkin kasar ya ce ba zai sake zuwa wata kasa da t adauki matakan hana 'yancin walwala ga 'yan kasar ta Qatar ba.
"Wanann shi ne babban ci gaba da muka samu kawo yanzu", inji wani babban jami'in gwamnatin Amurka yayin wata hira da yayi da mujallar Walla Street ta kasar.
"Ba cewa aka yi za su koma masoyan juna ba kai tsaye, har su zama manyan kawayen juna, amma dama ce gare su ta yin aiki tare da juna."










