Joe Biden: Trump ya yi wa hukumomin Amurka 'gagarumin ta'adi'

Asalin hoton, Reuters
Hukumomi masu matuƙar muimmanci ga tsaron Amurka suna cikin wani 'mawuyacin hali' a hannun gwamnatin Mista Trump inji zababben shugaba Joe Biden.
Mista Biden ya ce ya ce ba a ba shi bayanan da yake bukata, ciki har da bayanai daga ma'aikatar tsaro kan batutuwan tsaron ƙasa a wannan lokacin da yake shirin karban ragamar mulki.
Ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi da masu yi masa hidima kan tsaron cikin gida da harkoki da kasashen waje.
Ranar 20 ga watan Janairu Mista Biden zai zama shugaban ƙasa amma Shugaba Trump ya ki amincewa da shan kayen da yayi a hannun Joe Biden.
Kuma mako uku bayan da aka kammala zaben, hukumomi sun ki ba Mista Biden bayanan da akan ba zababben shugaban ƙasa, wanda yana da muhimmanci wajen sanar da shi halin da kasar ke ciki.
Amma muƙaddashin sakakataren tsaro Christpher Miller ya ce ma'aikatan da ke karkashinsa na sauke nauyin da aka dora mu su ba tare da nuna sakaci ba, kuma su na taimaka wa shirin muka mulkin.
"Ma'aikatar tsaro ta yi ganawa 164 da ma'aikata fiye da 400 kuma ta mika fiye da shafi 500 na takardu - wadanda suka zarce yawan takardun da ma'aikatan Mista Biden suka buƙata.
A cikin jawabinsa wanda ya wallafa a Twitter, Mista Biden ya ce shi da ma su yi ma sa hidima 'na fuskantar cikas' a ma'aikata tsaro da kuma a ofishin gudanarwa da kasasfin kudi.
"A yanzu ba ma samun cikakkun bayanan da muke bukata daga gwamnati mai barin gado kan muhimman wurare," inji shi.
"A ganina, wannan tamkar sakaci da aiki ne."











