Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus variant: Kasashen duniya na fargabar sabon nau'in kwayar Covid-19
Ƙasashe masu yawa na bayyana fargaba kan bayyanar wani sabon nau'i na kwayar cuta ta korona a Birtaniya, har ta kai ga sun fara hana matafiya daga can shiga ƙasashensu.
Fiye da ƙasashe 40 sun dauki matakin hana matafiyan Birtaniyan zuwa ƙasashen nasu yayin da Tarayyar Turai ke duba tsari na bai ɗaya da za ta ɗauka kan Birtaniyar.
Sweden ta hana matafiya daga ƙasar Denmark shiga ƙasarta bayan da aka gano sabon nau'in kwayar cutar ta korona a can.
Wannan sabon samfurin na da saurin yaɗuwa, amma ba a tabbatar ko yafi saurin lahana waɗanda suka kamu da shi ba.
Yayin da ake samun karuwar kasashe da ke hana matafiya daga Birtaniya shiga kasashen nasu, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta nemi sanar da duniya yadda ainihin lamarin yake.
Shugaban sashen samar da taimakon gaggawa na hukumar Mike Ryan ya ce kowace kwayar cuta na sauyawa daga nau'i zuwa nau'i, kuma wannan ba yana nufin tafi karfin masana kiwon lafiya ne ba.
Yadda lamarin yake a wasu sassan duniya
Ƙasashe masu dama daga Indiya zuwa Iran da Kanada duka sun hana matafiya daga Birtaniya shiga ƙasashensu.
Sai dai Amurka ba ta dauki matakin ba, amma wasu kamfanonin jiragen sama biyu - British Airways da Delta - ba za su bar matafiya su shiga jiragensu ba sai sun nuna shaidar ba sa dauke da kwayar cutar.
Saudiyya da Kuwait da Oman sun rufe dukkan iyakokinsu ga dukkan matafiya daga dukkan kasashen duniya.
Ban da ƙasar Denmark, an gano wannan sabon nau'in kwayar korona a Ostreliya da Italiya da kuma Netherlands.