Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid: Ireland, Italiya, Belgium da Netherlands sun haramta zuwan jirage daga Birtaniya
Kasashen Turai da dama sun haramta, ko kuma suna shirin hana jiragen da suka taso daga Birtaniya shiga cikinsu da zummar hana yaduwar wani sabon nau'i na cutar korona.
Netherlands da Belgium sun dakatar da jiragen Birtaniya sauka, yayin da Italiya za ta bi sahu. Kazalika an dakatar da jiragen kasa daga Birtaniya zuwa Belgium.
Ana sa rai Ireland za ta takaita tashin jiragen sama da kuma jigilar jiragen ruwa daga karfe 12 na daren Lahadi. Faransa da Jamus na cikin kasashen da ke duba yiwuwar daukar irin wannan mataki.
Sabon nau'in cutar ta korona ya yaɗu cikin sauri a Landan da kuma Kudu maso Gabashin Ingila.
Firaminista Boris Johnson ya saka sabbin dokokin kulle na mataki na huɗu masu tsauri, har ma aka fasa yin sassauci kan shirin bikin Kirsimeti, wanda gwamnati ta yi alƙawari a baya.
Manyan jami'an lafiya sun ce babu wata shaida da ke nuna cewa sabon nau'in ya fi barazana, ko kuma ba ya jin riga-kafi, sai dai kashi 70 cikin dari ya fi yaduwa.
Wadanne kasashe ne suka dauki mataki?
Sa'oi kadan bayan Birtaniya ta sanar da sabon nau'in cutar ta korona, Netherlands ta ce za ta haramta dukkan jiragen sama na fasinja daga Birtaniya shiga cikinta daga karfe shida na safe na Lahadi sai ranar 1 ga watan Janairu.
Za mu jira sai an samu "karin bayani mai girma" kan halin da ake ciki a Birtaniya, a cewar gwamnatin Netherlands, tana mai karawa da cewa za ta dauki mataki "na rage tasirin sabon nau'in cutar korona a Netherlands yadda ya kamata".
Ranar Lahadi kasar ta bayar da rahoton karin sabbin mutane 13,000 da suka kamu da cutar korona - duk da dokar kullen da ta sanya ranar 14 ga watan Disamba.
Belgium ta dakatar da jiragen sama da na kasa da suka fito daga Birtaniya daga shiga cikinta daga tsakiyar daren Lahadi. Firaiminista Alexander De Croo ya shaida wa gidan talbijin na Belgium VRT cewa haramcin zai ci gaba da aiki akala tsawon awa 24 a matsayin "kandagarki", yana ma karawa da cewa "za mu duba nan gaba mu ga idan akwai buktar daukar karin matakai".
Ministan harkokin wajenItaliya Luigi Di Maio ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa gwamnati na shirin daukar mataki na dakatar da jirage shiga kasar daga Birtaniya.
A kasar Ireland, gwamnati ta yi tattaunawar gaggawa kuma Ministan Lafiya Stephen Donnelly ya ce yana sa ran za a dauki mataki nan gaba a yau Lahadi kan sabbin tsare-tsaren jirage daga Birtaniya.
Zaa takaita shigar jiragen sama da na ruwa daga tsakar daren Lahadi, ko da yake ana ci gaba da daddale matakin da za a dauka. Ana sa ran matakan za su ci gaba da aiki tsawon kwana biyu kafin a yi nazari a kansu.
A Jamus, kakakin gwamnati Martina Fietz ta ce kasar tana duba yiwuwar takaita shigar jirage daga Birtaniya, inda ake tsara yadda matakin zai kasance.
A Faransa, tashar talbijin ta BFMTV reta rawaito cewa gwamnati na duba yiwuwar dakatar da jiragen sama da na kasa daga Birtaniya shiga cikinta, kuma gwamnatin na "duba yiwuwar hada kai daga kasashen Turai".
Ministar harkokin wajen Sifaniya Arancha González ta ce kasar tana son shigewa gaba domin sanya Tarayyar Turai ta dauki mataki kan batun.
Austria tana shirin haramta jirage daga Birtaniya zuwa kasar, inda yanzu haka take tsara yadda za ta aiwatar da matakin, a cewar kafafen watsa labaran Austria.