Covid-19: Abin da muka sani kan sabon nau'in cutar korona na Birtaniya

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
Ana danganta sabon nau'in cutar korona da ke ci gaba da yaduwa da sabbin jerin dokoki masu tsauri da aka kafa na hana yaduwar cutar a Birtaniya da Scotland da kuma Wales yayin bukukuwan kirsimeti, abin da ya kara jefa jama'a cikin tsanani da takura.
Ta yaya nau'in cutar da babu shi a da ya zamo wanda aka fi sani cikin watanni biyu kacal?
Masu bai wa gwamnati shawara kan yaduwar cututtuka sun ce suna tunanin cewa nau'in cutar ya fi yaduwa kan sauran.
Sun ce da farko abin ya fi bayar da tsoro, saboda yadda yake kunshe da wasu abubuwa da yawa masu rikitarwa.
Kamar yadda na sha rubutawa a baya, kwayar cuta na sauyawa a jikin mutum, don haka yake da muhimmanci a lura da yadda cutar ke sauyawa din.
Me yasa wannan nau'i ke tayar da hankalin jama'a?
To akwai wasu abubuwa uku da ke tattare da hakan. wadanda su ne suke jan hankali.
1.Shi wannan nau'i na saurin sauyawa a jikin mutum
2.Sannan yana da damar isa sassan jiki baki daya
3.Sakamakon bincike zuwa yanzu ya kuma nuna cewa wasu daga cikin sassan jikin da sabon nau'in zai iya shafa har da wasu kwayoyin halittun mutum.
Don haka dukkanin wadannam abubuwa sai suka taru wuri guda kan wata kwayar cuta da ke bazuwa a cikin jama'a kamar wutar daji.

Asalin hoton, Getty Images
Ya saurin yaduwarsa yake?
An fara gano shi ne a watan Satumba, a watan Disamba sai ya zamana cewa kusan kaso daya bisa hudu na wadanda suka kamu da cutar a Birtaniya duk nau'in ne da su, adadin da ya kai har zuwa kashi biyu bisa uku a watan Disamba.
Zo ka ga yadda nau'in ita wannan cuta ya shata layi cikin sakamakon da ake samu na wadanda suka harbu da korona.
Masu lissafi na tantance adadin wadanda suka kamu da nau'in cutar korona daban-daban a wannan hali da ake ciki.
Alkaluman da firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayar na nuna cewa mai yiwuwa ne adadin wadanda ke kamuwa da nau'in cutar ya kai kusan kashi 70 cikin 100 nan ba da jimawa ba.
Sai dai har yanzu akwai sauran ayar tambaya dangane da batun cewa ko ta fi sauran dukkan nau'ikan cutar yaduwa.
Wane nisa ta yi?
Ko dai sabon nau'in cutar ya bulla ne a jikin wani marar lafiya a Birtaniya, ko kuma an shigar da shi ne daga wata kasa, inda ba a iya bibiyar cutar ta korona sosai kamar yaddda ya kamata.
Ana iya samun sabon nau'in cutar a dukkanin sassan Birtaniya, ban da Ireland Ta Arewa.
Wasu bayanai daga Nextstrain da ke bibiyar sabon nau'in cutar sun nuna cewa akwai ta a kasashen da suka hada da Denmark da Australia, kuma dukkaninsu an kai can ne daga Birtaniya.
An kuma ga wani sabon nau'in cutar mai kama da wannan a Afrika Ta Kudu.
Daga ina sabon nau'in cutar ya samo asali?
A gaskiya nau'in cutar na sauyawa sosai ma kuwa.
Bayanin da aka fi gamsuwa da shi shi ne sabon nau'in ya bulla ne daga wata mara lafiya da garkuwar jikinta ta yi rauni har ta kai ga ta kasa dakile cutar.
Don haka sai jikinta ya zamarwa sabon nau'in cutar kamar wata sheka, inda ya rika bunkasa yana kuma hayayyafa.
Shin ya kan iya kisa?
Babu wata hujja da ke nuna cewa hakan na faruwa, duk da yake ana bukatar a rika bibiyarsa.
Sai dai, karuwar wadanda ke kamuwa da nau'in cutar na iya janyo yawan wadanda ake kwantarwa a asibiti.
Shin riga-kafi zai iya yaki da wannan nau'i na korona?
Kusan a iya cewa Eh.., domin dukkanin riga-kafin da aka samar guda uku na da wasu sinadarai da ke bai wa mutum kariya daga kamuwa da cutar da ke ci gaba da yaduwa a yanzu.
Su wadannan riga-kafi suna horar da garkuwar jikinka ne game da yadda za ta yaki cututtukan da ke neman shiga jikinka, don haka ko da cutar ta sake rikida sabanin yadda aka santa, riga-kafin zai ci gaba da yakarta babu kakkautawa.










