NIMC: Yadda mutum zai yi rijistar katin zama ɗan ƙasa a Najeriya

Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayar da umarnin rufe duk wani layin waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN ba ko da tsoho ne.

Hukumar ta bayar da wa'adin makonni biyu ga masu layin waya waɗanda ke da wannan lambar ta NIN da su kai ta ga kamfanonin sadarwar da suke da rajista da su domin a yi musu rajistar lambar da layin wayarsu.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta bayar da umarnin sayarwa ko rajistar da sabbin layin waya a ƙasar.

Ga wasu daga cikin matakan da hukumar ta ɗauka domin tabbatar da wannan dokar:

  • Tabbatar da cewa duka kamfanonin sadarwa sun bi umarnin farko na dakatar da rajistar sabon layin waya.
  • Kamfanonin sadarwa su buƙaci duka masu amfani da layukansu su bayar da sahihiyar lambar shaidar ta NIN domin haɗa ta da layinsu.
  • An bai wa masu amfani da layukan waya wa'adin mako biyu su kai lambar NIN ɗinsu (daga 16 ga watan Disamban 2020 zuwa 30 ga watan Disamban 2020).
  • Duka layukan wayar da ba a yi musu rajista da lambar NIN ba nan da mao biyu za a rufe su.
  • Kwamiti na musamman ciki har da minista da wasu manya za su kasance masu sa ido domin tabbatar da kamfanonin sadarwa sun bi wannan umarni.
  • Karya wannan doka za ta jawo a ɗauki mataki, ciki har da yiwuwar ƙwace lasisin kamfani

Ta yaya mutum zai duba lambarsa ta NIN daga wayarsa?

Mutum zai iya duba lambarsa ta NIN ta hanyar latsa wasu lambobi a wayarsa.

Hukumar da ke rajistar katin ɗan ƙasa wato NIMC ta ce mutum zai iya latsa *346# domin samun lambarsa.

Masu amfani da layukan MTN da Airtel da 9mobile da Glo duk za su iya duba wannan lambar.

Ta yaya za ku yi rajistar katin zama ɗan ƙasa?

Ga waɗanda ba su da wannan lambar ta NIN, a sauƙaƙe za su iya bin waɗannan matakan domin samun lambarsu.

Mataki na ɗaya

  • Za ku iya ziyartar wannan shafin - https://penrol.nimc.gov.ng/loginForm.tpl.html.php domin ku cike fom ɗin rajistar.
  • Ku cike duk wani gurbi da aka buƙaci ku cike a fom ɗin
  • Bayan kun cike sai ku sauke fom ɗin da kuka cike ku gurza shi domin samun kwafi.

Mataki na biyu

Kai fom din rijistarku ofis

  • Za ku iya tafiya domin zuwa wurin rajistar katin ɗan da ke kusa da ku da sahihan takardunku.
  • A ofishin rajistar, za a nuna muku jami'in da za ku je wurinsa domin tantance duk wasu bayanai da kuka cike da kuma sahihan takardunku.
  • Idan komai ya tafi daidai, za a ɗauki hoton yatsun hannayen ku, duka guda goma, bayan nan za a baku wata takardar da za ta kasance a matsayin shaidar kun yi rijista.

Mataki na uku

Karɓar lambarku ta NIN

  • Wa'adin kwanakin samun lambar NIN bai wuce tsakanin kwanakin aiki biyu zuwa uku ba, bayan kun kammala rajistar ku.
  • A wani lokacin kuma samun wannan lamba ta NIN na ɗaukar lokaci sakamakon ƙoƙarin tantance bayanai.
  • Ya kamata mutum ya adana takardar da aka ba shi ta shaidar yin rajista domin za a buƙaci takardar idan mutum zai karɓi lambarsa.