Aisha Buhari: Shin Uwargidan Buhari ta koma Dubai da zama?

Asalin hoton, AISHA BUHARI FACEBOOK
- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Lokacin karatu: Minti 3
Jama'a da dama na tafka muhawara a shafin Twitter da wasu kafofin sada zumunta, tun bayan da wasu kafofin watsa labarai suka ruwaito cewa Uwar Gidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta koma Dubai da zama.
Tun da farko dai kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ce ta kawo labarin, inda ta ce Aisha ta koma Dubai ne saboda rashin tsaro.
Kafafen watsa labaran da suka kawo wannan labarin sun ce tun bayan bikin 'ƴar shugaban, wato Hanan, Aisha Buharin ta bar Najeriya.
Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa har ta kai ga kalmar "Dubai" ta zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake tattaunawa a Najeriya, inda wasu daga cikin 'yan ƙasar ke tambaya ina za su gudu su je idan matar shugaban ƙasa ta gudu?
Gaskiyar lamari

Asalin hoton, Aisha Buhari
Kafar yaɗa labaran Sahara Repoters ta ruwaito cewa tun a watan Satumba Aisha ta bar Najeriya, amma hakan ba gaskiya ba ne, domin ko a ranar 1 ga watan Oktoba, ranar da aka yi cikar Najeriya shekara 60 da samun 'yancin kai, sai da aka ga Aisha cikin kaya masu launin tutar Najeriya.
Don tabbatar da iƙirarin da wasu kafafen watsa labarai suke yi kan wannan lamari, BBC ta yi bincike inda majiya mai ƙarfi daga fadar shugaban ƙasar ta tabbatar mana da cewa uwar gidan shugaban Najeriyar tana birnin Dubai.
Majiyar da ta tabbatar mana da cewa uwargidan ba wai ta koma Dubai da zama na dindindin ba ne kamar yadda wasu ke iƙirari, amma dai ta je can ne neman magani.
Sai dai majiyar tamu ba ta shaida mana ranar dawowar uwargidan shugaban ƙasar ba.
Ko a kwanakin baya ma lokacin da ake tsakiyar annobar korona sai da Aisha Buharin ta tsallaka zuwa Dubai don neman magani, inda a hanyar dawowarta, jirgin fadar shugaban ƙasar ya samu matsala.
Ko Aisha ta damu da matsalar tsaron Najeriya?
Da alama matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da Aisha Buhari ta yi ta yin shaguɓe a kansu a kwanakin baya, inda ta yi ta kira da a kawo ƙarshen matsalolin da ke faruwa a arewacin Najeriya.
A ranar 17 ga watan Oktoban bana, Aisha ta wallafa wani saƙo a shafukanta na sada zumunta da taken "A ce ci jama'a", inda ta bi sahun masu kira a kawo ƙarshen rashin tsaron da ke addabar Arewacin Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Saƙon na ƙunshe da wata wakar mawaƙin Kannywood, Adam A. Zango inda yake kokawa kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin Najeriya.
Washe gari kuma a ranar 18 ga wata sai ta sake wallafa wasu saƙonni da taken "Arewa mu farka", biyu daga ciki bidiyo ne ɗaya kuma hoto ne, amma dukansu saƙon su kan kishin ƙasa ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Ko a shekarar 2019, sai da Aisha Buharin ta shirya taron addu'o'i na musamman da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa domin neman agajin Ubangiji game da tarin kalubalen da kasar take fuskanta.

Asalin hoton, FACEBOOK/AISHA BUHARI
Taron dai ya haɗa malamai daban-daban daga ƙungiyoyin Izala da na Ɗariƙa.











