GSS Ƙanƙara: Boko Haram ta ɗauki alhakin sace ɗaliban makarantar

Shekau

Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da wani saƙon murya inda ta yi ikirarin cewa ita ce ta sace ɗaliban sakandaren Kankara da ke jihar Katsina.

Sakon da shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya fitar na tsawon minti 4:30, ya zo bayan kwana uku da sace ɗaliban su fiye da 500 abin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar baki ɗaya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriyar ta ce 'ƴan fashin da suka sace ɗaliban makarantar sakandaren kimiyyar ta Ƙanƙara sun tuntuɓi hukuma kuma tuni an fara tattaunawa kan abin da ya shafi tsaron yara da yadda za a mayar da su gida lafiya.

Tun da fari hukumomi sun ɗora alhakin sace ɗaliban kan 'yan bindiga.

Gwamnatin jihar Katsina ta ce har yanzu akwai fiye da ɗalibai 300 da ke hannun 'yan bindigar, bayan da wasu suka kuɓuta.

Kazalika Gwamna Masari na Katsina ya je Daura domin ya yi wa shugaban ƙasa ƙarin bayani kan halin da ake ciki dangane da ƙoƙarin da ake yi na gano ɗaliban da aka sace.

Kazalika gwamnan ya sanar da shugaban ƙasar cewa hukumomin tsaro sun gano inda yaran suke a hannun maharan.

President Muhammadu Buhari and Governor Aminu Bello Masari

Asalin hoton, Garba Shehu

Bayanan hoto, Shugaba Buhari (Hagu) ya karbi bakuncin gwamnan Katsina Masari

Me masana ke cewa game da wannan batu?

Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike ne kan harkokin ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi a yammacin Afirka, ya shaida wa BBC cewa ba abin mamaki ba ne idan har iƙirarin Boko Haram ɗin ya kasance gaskiya bisa la'akari da cewa a kwanakin baya Boko Haram ta ce ta kutsa cikin yankunan arewa maso yammacin Najeriyar.

Baristan ya ce "Yan Boko Haram a watannin baya sun fito sun ce sun wanke kan 'yan bindiga inda suka haɗe suke aiki tare".

A cewarsa, idan ta tabbatar cewa Boko Haram ce ta sace ɗaliban "mafita kawai ita ce sojoji da sauran jami'an tsaro su yi duk abi da za su yi su tabbatar sun cece su tun da gwamnati tana da'awar cewa ta kewaye inda ake zarrgin an rike yaran."

"Idan ba haka ba abubuwa biyu ne za su faru: idan Allah Ya sa an samu sauki za su buƙaci kuɗi ne da kuma 'yan uwansu da ke cikin kurkuku... idan kuma ba a yi sa'a ba idan aka yi wasa za su halaka yaran nan ne,' in ji Bukarti.

Wanne hali iyayen ɗaliban ke ciki?

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a da daddare

A halin da ake ciki dai iyayen ɗaliban da aka sace na ci gaba da roƙon hukumomi su yi dukkanin mai yiwuwa domin ceto mu su ƴaƴansu, da har kawo yanzu basu dan halin da suke ciki ba tun bayan sace su.

Mahaifin wasu ɗalibai biyu ya shaida mana cewa tun da lamarin ya faru suke cikin damuwa "domin duk lokacin da aka ce yaronka ya ɓata dole ka shiga damuwa, don gara ma a ce mutuwa ya yi."

Ya ce mahaifiyar yaran ta shiga damuwa sosai ko da yake sun fawwala komai ga Allah.

Sai dai wani abu da ya ja hankali shine na tarwatsa iyayen yaran da suka taru a makarantar da jai'an tsaro suka yi, ta hanyar sanya musu barkonon tsohuwa, abin da wasu daga cikin yan kasar suka yi Allah wadai da shi, ciki har da jam'iyyar PDP da ta kira matakin a matsayin abin kaico. ''A dake ka, kuma a hana ka kuka", in ji PDP.

Shi dai gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, wanda ya ziyarci makarantar ranar Asabar, ya bayar da umarnin rufe ɗaukacin makarantun sakandare na kwana da ke faɗin jihar.

Sannan ya ce a halin da ake ciki jami'an yan sanda da sojoji da ma na hukumar tsaron farin kaya sun duƙufa domin gano inda daliban suke tare da tseratar da su lami lafiya.

Makarantar Sakandiren Kankara