Majalisa ba ta da hurumin gayyatar Buhari kan tsaro – Malami

Abubakar Malami

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Antoni Janar ɗin ya ce shugaban ƙasa yana da cikakken iko da sirri kan abin da ya shafi tsaro. Wannan wani ƙarfin iko ne da dama da yake da su shi kaɗai

Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami, ya ce majalisar dokokin ƙasar ba ta da hurumin gayyatar Shugaba Muhammadu Buhari kan batun tsaro.

Malami ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, kwana guda kafin shugaban ƙasar ya bayyana a gaban majalisar don amsa tambayoyi kan sha'anin rashin tsaro da ake ciki a ƙasar.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin ta buƙaci Buharin ya je gabanta don yin bayani kan matakan da yake ɗauka a harkar tsaron, bayan da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka kashe manoma fiye da 70 a garin Zabarmari da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.

A sanarwar da ya fitar, Malami ya ce bai kamata a bayyana sirrin salon yaƙi da ta'addanci da gwamnati ke yi ga kowa da kowa ba.

"Bai kamata a bayyana irin tsare-tsare da matakan da shugaban ƙasa kuma babban kwamandan askarawan Najeriya ke bi ga mutane ba, la'akari da tasirin tsaro saboda zai iya yin illa ga yaƙin da ake yi da ta'addanci," kamar yadda sanarwar ta ce.

Antoni Janar ɗin ya ce a matsayinsa na babban kwamandan askarawan Najeriya, shugaban ƙasa yana da cikakken iko da sirri kan abin da ya shafi tsaro. Wannan wani ƙarfin iko ne da dama da yake da su shi kaɗai.

"Don haka kiran shugaban ƙasar kan batun tsaron ƙasa, majalisar wakilan tana wuce makaɗi da rawa ne kan abin da kundin tsarin mulki ya shata mata," a cewarsa.

Wannan layi ne

Nasara a yaƙi da ta'addanci

Sanarwar ta Malami ta jinjinawa Shugaba Buhari da cewa ya samu gagarumar nasara wajen hana tashin bama-bamai da kashe-kashe da lalata rayuka da dukiyoyin jama'a idan aka kwatanta da halin da ƙasar yake ciki lokacin da ya karɓi mulki a shekarar 2015.

"Duk da cewa batun yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara wajen ƙwato ƙananan hukumomi 14 da a baya suke ƙarƙashin ikon Boko Haram a arewa maso gabas bayyanannen abu ne, amma ba a bayyana wa al'umma matakan da aka bi wajen cimma wannan nasara ba."

"A yayin da yake miƙa ta'aziyyarsa da jajantawa waɗanda duk wata matsalar tsaro ta taba shafa kai tsaye a ƙasar, antoni janar ɗin ya ƙara jaddada cewa batun tsaron ƙasa ba abu ne da za a yi ta yamiɗiɗi da shi ba.

"Sannnan bai kamata a bayyana tsarin da ake bi wajen tsron ƙasar ba kawai don neman suna," in ji Malamin.

Ya ƙara da cewa: "Kundin tsarin mulkin kasar ya yi wa Shugaba Buhari shinge daga bayana wasu sirrika da suka shafi ofishinsa game da sha'anin tsaro, wanda yake da matuƙar muhimmanci.

"Majalisar dokoki ba ta da hurumi a kundin tsarin mulki na yin tantamar wani yanayi da har za ta gayyaci shugaban ƙasa zaurenta kan ayyukan da suka shafi amfani da dakarun tsaro.

"Shugaban ƙasa ne yake da hurumin bayyana a gaban majalisar dokoki a lokacin da yake son bayyana mata wai abu ba wai majalisa ta gayyace shi ba," a cewar Malami.

Ƙarin labarai masu alaƙa

Wannan layi ne

Gayyatar da majalisa ta yi wa Buhari

A ranar Talata 1 ga watan Disamba ne majalisar wakilan Najeriyar ta gayyaci Shugaban Buhari zaurenta domin ya yi mata bayani kan matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.

Ƴan majalisar sun yanke shawarar gayyatar Shugaba Buhari ne bayan kisan da aka yi wa wasu manoma fiye da 43 a kauyen Zabarmari na jihar Borno.

Majalisar ta ce akwai buƙatar shugaban ya yi bayani a kan abin da ya hana karya-lagon mayaƙan Boko Haram duk kuwa da irin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a kan jami'an tsaro.

Honourable Satomi Ahmed, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin, ya shaida wa BBC cewa an ɗau wannan mataki ne ganin cewa an sha kiraye-kiraye ga shugaban kan neman sake fasalin harkokin tsaro amma babu shiru ake ji.

Satomi ya ce yanayin da ake ciki ya tabbatar da cewa dole ana neman gyara, amma a iya sanin majalisa ta rasa dalilan shugaban ƙasa don haka ta buƙaci ya bayyana a gabanta.

Kwanaki kaɗan bayan gayyatar ne sai Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa Shugaba Buhari ya amince ya bayyana a gaban majasalisar domin amsa tambayoyi kan matsalolin tsaron Najeriya.