Falasɗinu : Dakarun Isra'ila sun kashe matashi Bafalasɗine

Asalin hoton, Reuters
Jami'an Falasɗinu sun ce wani matashi ya mutu bayan da aka harbe shi yayin artabu da jami'an tsaron Isara'ila a gaɓar yammacin Kogin Jordan.
Ma'aikatar Lafiya ta ƙasar ta ce Ali Ayman Abou Aliya wanda ake kyautata zaton shekarunsa 16 ya mutu a gadon asibiti, inda yake jinya sakamakon shiga jikinsa da harsashi ya yi.
Dakarun Isra'ila sun musanta amfani da harsashi mai kisa a yayin artabu da masu zanga-zangar Falasɗinawa da ke jifa da duwatsu.
Wani mai magana da yawun sojin Isrra'ila ya ce ba shakka an yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar, kuma daga cikin matakan da aka yi amfani da su har da harba musu harsashin roba.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Gabas ta Tsakiya, Nickolay Mladenov, ya ce ya kadu matuka da kisan.
Dubban mutane na gudanar da zanga-zanga a Gaza, domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yankin gaɓar yamma da Kogin Jordan.
Masu boren na ɗaga tutocin Falasdinawa, suna kuma yin Allah wadai da Shugaba Trump na Amurka kan goyon bayan da ya nuna ga shirin Isra'ilar.
Shi ma Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya gargaɗi Isra'ila da ta watsar da shirin nata da ake hangen zai tayar da sabon rikici a yankin.
Wakilin BBC ya ce kusan dukkan kawayen Isra'ila sun ce shirin na mamayar da take yi ba da yawun bakinsu ba. Dama kuma kasar na cikin rudun siyasa''.
To sai dai gwamnatin Benyamin Netanyahu ta ce a ranar Laraba ne za ta fara abin da ta tsara.










