Mamayar Isra'ila: Abin da kuke buƙatar sani kan mamayar Isra'ila a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Demonstrator carries a Palestinian flag at a protest in Tel Aviv against Israel's annexation plans (06/06/20)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Fira minista Benjamin Netanyahu ya ce matsugunan - da ke kan ƙasar da Falasɗinawa ke iƙirarin mallaka - za su zama ɓangaren Isra'ila
    • Marubuci, Daga Tom Bateman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 12

Fira ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai iya mamayar ƙwace wasu yankunan zirin Gaza da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a yanayin zafin bana.

A cewarsa, bisa la'akari da yunkurin shugaban Amurka Donald Trump na tabbatar da zaman lafiya a yankin, wannan wani al'amari ne da zai "buɗe sabon babi a tarihin aƙidar Yahudanci ta Sahayoniya."

Falasdinawa sun tsaya ba gudu, ba ja da baya cewa za su fice daga duk wata yarjejeniya da aka ƙulla a baya, tare da kasadar kassara gwamnatinsu da ba ta da karfin iko.

A wajensu, wannan yunkurin zai haifar da asarar muhimmin yankin ƙasar, da kuma wargaza makomarta, ta hanyar dakushe ƙoƙaarin cimma burinsu na kafa ƙasa mai 'yancin cin gashin kanta.

Mafi yawan ƙasashen duniya na cike da alhinin nuna damuwar keta haddin dokokin duniya ƙarara, tare da gargaɗin "zafafar al'amura" da kuma ruruwar wutar rikici.

Shin ko akwai wani shirin da aka shimfida da manufar kyautata al'amura, kan doron wani muhimmin tsari a yankin da za a gudanar na tsawon shekaru?

"A yi abin da ya dace!"

Na fara tafiya ne a kan babban titin da ke kudancin wajen birnin Ƙudus. Titin an yi masa lakabi ne da sunan Menachem Begin, tsohon ɗan tawayen shugaban Yahudawa, da ya taba zama fira ministan Isra'ila na shida.

Ya kasance wani jigo na masu tsananin kishin ƙasa, inda ya kafa ƙungiyar da ta rikiɗe ta zama jam'iyyar siyasa ta Likud, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Benjamin Netanyahu.

Wannan babban titi na da tudu mai nisan kai wa ga tsawon bene mai hawa 12 da ke like da manyan hotunan Mista Netanyahu da Shugaba Trump.

"Ba za a kafa ƙasar Falasdinawa ba!" wani take da aka kambama cikin harshen Hebrew. "'Yancin kai da ƙarfin ikon mulki - a yi abin da yake daidai!"

Wannan sako ne ba wai daga shugabanni Isra'ila da Amurka na yanzu ba. Ya fito ne daga rukunin shugabannin da ke jan ragamar wuraren da Yahudawa suka mamaye a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan - yankin da suke gani a addinance mallakarsu ne.

Yochai Damri, head of the Har Hebron Regional Council, shows a map of what Israeli settlers say is a map of a Palestinian state under Donald Trump's peace plan (03/06/20)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan kama-wuri-zauna sun ce kafa wata ƙasar Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan abu ne da zai zamo wata barazana

Magaddan gari a yanki na iƙirarin cewa Isra'ila ce ke da ikon mallakar sama da kashi 30% na fadin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kamar yadda Mista Trump ya gabatar gaban teburin sulhu.

Yayin da Mista Netanyahu kuma nan ba da daɗewa ba zai iya gabatar wa majalisar ministocinsa ko majalisar ƙasa ƙudurorin "tabbatar da aiki da dokar Isra'ila" a kan karɓe yankunan, magaddan gari na kawo cikas ga ikonsa a siyasance.

Wannan alama ce da ke nuna yadda wannan takaddama ta rincaɓe a Isra'ila tsawon shekaru.

'Kayan marmarina ba na Trump ba ne da zai bayar'

A tsakanin itatuwan ruman da bishiyoyin zaitun, Mohammed Yehya Ayer ya nuna mini gonarsa.

Muna gefen ƙauyen Irtas na Falasdinawa. Akwai launuka da alamomin da ke nunin al'amuran rayuwa da aka saba da su cikin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Rufin gidaje masu rawaya a daukacin tsaunukan da ke kudu maso yammacin yankin - kyakkyawar unguwar Efrat ce ta matsugunan da Isra'ila ta fitar gwanin ban sha'awa.

Mohammed Yehya Ayer
Bayanan hoto, Mohammed Yehya Ayer ya ce yankunan Gaɓar Yamma "ai tuni ma kamar an haɗe su ne"

Bayan shingen yankin, ƙasar ta malala har zuwa gaɓar wani kwari da ba komai cikinsa, a wani wurin wasan kwallon gulf da ke dankare da konannen juji rawaya-rawaya da duwatsu, kafin a fara gina gidaje a wajen.

Tubula launin toka-toka na Dheisheh, wadanda aka kafa kyakkyawan matsugunin 'yan gudun hijira a gefen birnin Bethlehem na al'ummar Falasdinawa.

Na tambayi Mohammed ko me yake gani game da kalaman Mista Netanyahu na baya-bayan nan.

"Ba wani abu suke nufi ba," kamar yadda ya faɗa mini. "Wadannan yankuna tuni aka mamaye su.. Duk a hannunsu suke." Haka dai Mohammed ya ci gaba da bayyana ra'ayinsa.

Zuri'arsa sun daɗe suna noma a wannan ƙasa tsawon zamani. Bayan da aka kafa matsugunnin Efrat cikin shekarun 1980, al'amura suka fara sauyawa. Ya dai kwatanta yadda ake ta fafutukar samun karfin ikon mallakar yankin.

"Da na aza tubali 10 a nan (don yin gini), sai mahukuntan Isra'ila su zo su rushe," in ji shi.

"Isra'ilawa.. kan bijiro da shawarwari sannan su kwace ɗumbin faɗin ƙasa ta hanyar fakewa da cewa ta hukuma ce... kuma gwamnati na taimaka wa 'yan kama-wuri-zauna."

Map of the West Bank settlements
Presentational white space

Isra'ila na shirin kafa wani sabon matsugunnin da aka yi wa lakabin Givat Eitam, a arewa maso gabas daga inda muke tafiya tare da Mohammed. Kuma zai kasance yana da kusanci da Efrat.

Gonar Mohammed dai tana nan a tsakanin wadannan wurare biyu. "Idan an gina Efrat ta hanyar tursasawa, suna iya kafa ƙatuwar ƙofa da shinge, ta yadda ba za a bari mu shiga gonakinmu ba," a cewarsa.

"Za su umarce mu, mu riƙa neman izini da amincewar hukuma tukunna."

Mahukuntan Isra'ila akai-akai sukan yi nuni da cewa za a iya ƙalubalantar hanyoyin da aka katange wajen ayyukan tsare-tsare ko a kotuna.

Sai dai sun ƙi cewa komai dangane da samun hanyar shigewa idan an ci gaba da aikin gina Givat Eitam. Alkalai sun kusa yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da aka yi kan rabon ƙasa don gina sabon matsugunnin.

Na nuna wa Mohammed cewa shirin Trump na nufin Falasdinawa za su samu kashi 70 cikin 100 na faɗin yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Kuma za a dakatar da aikin faɗaɗa gine-ginen matsugunni (na Yahudawa) har tsawon shekara hudu a wuraren da ke wajen yankunan da Isra'ila ta mamaye.

Shugaban Amurka ya wallafa wata taswira a shafinsa na twita ranar 28 ga watan Janairu, inda ya ce, "Wannan shi ne fasalin yadda ƙasar Falasɗin za ta kasance, tare da babban birninta a wasu sassan gabashin Ƙudus."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

Ya sake tsinko wani nunannen kayan marmari.

"Wane ne Trump da har zai alkawarta wani abu? Ko ƙasar tasa ce?" kamar yadda ya tambaya, yayin da yake riƙe da ɗan itaciyar gonarsa.

"Zan iya miƙa maka wannan ɗan itaciya kyauta saboda nawa ne. To idan ba ni na mallake shi ba fa, ta yaya zan iya yi maka kyautarsa?

'Sun ce Allah na tare da mu kuma za mu yi yadda muke so'

Wurin ba shi da nisa daga Efrat. Sai dai tafiyar ta yi nuni da cewa wurin ya yi matukar kama da Gaɓar Yamma.

Sign for Efrat settlement
Bayanan hoto, Efrat ɗaya ne daga cikin matsugunan Yahudawa fiye da 130 a yankin Gaɓar Yamma da aka mamaya

Kafin a wuce shingen jami'an tsaro, an kakkafa turakun kankare a gefen titi mai ƙura da ke nuni da yiwuwar Isra'ila ta faɗaɗa kewayen katanga, tare da shingayen bincike - almarin da ke nuni da shingen raba garin.

An fara ginin ne lokacin da Falasdinawa suka shiga zagaye na biyu a gwagwarmayarsu ta Intifada, tsakanin shekarun 2000 zuwa 2005, inda hare-haren ƙunar baƙin wake suka riƙa hallaka Yahudawa ba kakkautawa,

Lamarin da ya sa har Isra'ila ta kaddamar da farmakin mamayar biranen zirin Gaɓar Yamma. Isra'ila ta yi nuni da cewa shingayen katangar na ceton rayuka ne.

Sai dai masu sukar lamiri na nuna lamarin a matsayin dabarar mamayar ƙasa.

Ana ganin matsugunan Yahudawan sun ƙeta ƙa'ida a ƙarƙashin dokar ƙasashen duniya, tun daga kan al'amarin da ya shafi haramci ga kasashe su kwashi wani adadi na al'umma a killace su karkarshin kulawar rundunar sojoji.

Isra'ila ta yi watsi da wannan, inda ta dage kan cewa yankin "ana takaddama a kansa" saɓanin cewa an mamaye shi ne.

Jami'in tsaron soja dauke da makami ya daga mini hannu a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan titunan Efrat da ba kowa.

Shirin Trump ya yi matukar shan bamban da shirye-shiryen kawo zaman lafiya da aka gudanar a baya.

Wasu na hasashen cewa al'amarin na iya bayar da dama ga Isra'ila ta samu kaso mai tsoka na ko'ina a matsugunnan, tare da wurin da aka shata ginin Efrat, alal misali

A matsayin sassaucin yarjejeniyar da aka kulla da Falasdinawa, wadanda ke son ganin Zirin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ya kasance a ɓangaren ƙasar da suke burin kafawa.

Mafi yawan manyan gine-ginen tsugunnar da Yahudawa an yi su ne a tsakanin layukan da aka shata na sassan da ke karawa da juna, ko karkashin rundunar soja, wadda take tun kafin 1967.

Lokacin da aka fafata yaki tsakanin Larabawa da Yahudawa, yayin da Isra'ila ta samu galabar mamaye yankin Gaɓar Yamma daga hannun mahukuntan ƙasar Jordan.

Amma dai shirin Shugaba Trump na nuni da yiwuwar amincewar Amurka ga Isra'ila kan daukacin gine-ginen da ta yi, tare da sahale mata muhimmin tsaunin gaɓar Kogin Jordan - kafin ma a kulla wata yarjejeniyar warware takaddama da Falasdinawa.

'Tarihi ya nuna mallakarmu ne'

A wajen wata mashaya mai cike da hayagaga, na tattauna da Yedidia Mosawi da Sharon Barazani, wadanda daukacinsu suna da shekaru sama da ashirin.

Yedidia ya fada mini cewa yana aiki ne a matsayin jami'in tsaro ne, kuma ya fito ne daga wani matsugunni can kudu, wanda ke kusa da Hebron.

"Wurin na da ban sha'awa da kuma matuƙar muhimmanci ga Isra'ila," a cewarsa kan batun Gaɓar Yamma da Kogin Jordan - sunan yankin cikin harshen Hibru shi ne Judea da Samaria, kamar yadda Yahudawa da yawa ke kiransa

Sharon Barazani (left) and Yedidia Mosawi (right)
Bayanan hoto, Sharon Barazani da Yedidia Mosawi

Na tuntube shi game da shirin Mista Netanyahu. Sai ya nuna cewa abin da aka yi bai ma isa ba.

"[Kamata ya yi mu] shimfiɗa dokar Isra'ila a duk faɗin wannan ƙasa. Don tarihi ya nuna tamu ce. A wajen al'ummar Yahudawa yana da matukar muhimmanci - ba mu da wata ƙasa da ta fi nan."

Sharon ya ƙara da cewa: "Ba zai yiwu ka ce wa mutane su bar ƙasarsu, da gidansu ba."

Na isa ofishin magajin garin. A wajen harabar akwai duwatsun da ake adon bangon gini masu daɗɗaɗen tarihi da aka gano a ƙasar jordan tun cikin 1880.

.

Ana kiran wannan dutsen adon gine-gine da taswirar Madaba, wani hoto ne na Ƙasa Mai Tsarki tun cikin ƙarni na shida. Daya daga cikin rubuce-rubucensa cikin harshen Girka kusa da birnin Bethlehem, na kafa hujjojin littafin Baibul da inda Ephratah yake.

An dai kafa matsugunin Isra'ila na Efrat cikin 1983. Magajin garin Oded Revivi na sane da alaƙar ƙasar da addini da kuma aƙida, ko da yake a cewarsa, ba shi ne jigon tarewar mafi yawan 'yan kama-wuri-zaunan ba.

Mafi yawa daga cikinsu, tamkar dai yadda ya yi a shekarun 1990, sun zo ne saboda yiwuwar samun gidaje masu sauƙi a tsakanin al'ummar Yahudawa.

Oded Revivi
Bayanan hoto, Mayor Oded Revivi ya ce shirin Trump sahihin ƙoƙari ne na warware rikici

Mista Revivi ya tattauna Netanyahu. Ya kuma san jami'an da ke cikin ayarin shata iyakokin da ɗora wa alhakin yadda za a ɓullo wa aikin haɗe yankunan, kuma ya goyi bayan shirin Trump tun daga farkonsa.

"Ina jin cewa wani kyakkyawan yunƙuri ne bijiro da tunanin sabuwar hanyar warware rikici," in ji shi.

Ko mene ne ra'yinsa game da sauran magaddan garin da ke sukar fira minista, cewa Isra'ila na 'yancin ƙara haɗe yankunan Gaɓar Yamma? Mista Revivi ya gwale takwarorinsa cikin ladabi.

"Irin wannan tunanin yana zuwa ne saboda rashin fahimtar al'amuran duniyar da muke ciki," a cewarsa, yana nuni da gagarumar sukar da mafi yawan ƙasashen duniya ke yi ga duk wata mamaya.

"Tunanin cewa muna da ƙarfi da girma, kuma Allah na tare da mu, shi ya sa za mu yi abin da muke so."

Kuma akwai buƙatar a fahimci shirin Trump, mataki-mataki ne, a cewarsa. "Wannan shi ne matakin farko."

Haɓakar gine-gine

'Yan adawa dai na ganin shirin Trump ba wani abu ba ne illa kawai tabbatar da hakikanin abin da aka tsara a baya, kimanin tsawon rabin karni na keta dokokin ƙasashen duniya.

Na isa inuwar wata katuwar gada da ake ginawa - tare da rubanya fadin hanyar da ke kan babban titin Begin da ya mike kai-tsaye zuwa cikin yankin Gaɓar Yamma, inda ya haɗe birin Ƙudus da Efrat da kuma sauran matsugunnan da ke can a kudanci.

Bridge construction seen from Beit Jala
Bayanan hoto, Wata gada da ake ginawa da za ta sauƙaƙa zirga-zirga daga birnin Ƙudus zuwa yankunan matsugunan Yahudawa

Muna tsaye 'yan mitoci ƙlilan daga wani ɓangare na shinge da ya raba sassan - katanga ce ta kankare mai tsawon mita takwas (kafa 26) da ta kange mu daga gidajen Falasdinawan da ke ɗaya ɓangaren.

Daidai lokacin da motoci masu lambar Isra'ila ke kai-kawo ta kan gadar da ke samanmu.

Wannan shi ne "cikakken labarin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a tsawon shekara 53 da suka gabata," a cewar Dror Etkes, wanda ke tafi da wata ƙungiyar Yahudawa ta Kerem Navot

(Lambun inibin Navot - wani jigo da aka ambata a littafin Baibul, kuma an kashe shi ne a kan gonarsa), ƙungiyar dai tana bibiyar yadda gine-ginen matsugunnan ke tafiya.

"Lamarin dai tamkar karba ne daga hannun Falasdinawa a damƙa wa Yahudawa.

Yadda ake yi shi ne ƙwace ƙasa tare da ba da ita ga Yahudawa kawai. Wannan abu na farko ke nan. Wani abin kuma katangewa da kuma hana faɗaɗa yankunan al'ummar Falasdinawa," in ji shi.

Mun ga yadda ma'aikata daga Gabashin Turai ke ɗaukar ƙatoton ƙarfe.

Bridge construction workers
Bayanan hoto, Ayyukan raya ƙasa na fatan ganin bunƙasar al'umma a yankunan da ake ƙoƙarin mamayewa

Mista Etkes ya ce, wannan shi ne aikin gine-gine mafi girma da kasar Isra'ila ke yi a yankin Gaɓar Yamma cikin shekara ashirin.

Karin hanyoyi da kafa bututan ruwan famfo da mazurarin fitar bahaya da ake ginawa, in ji shi don samun damar bunƙasa rayuwar ɗumbin mutanen da za su tare.

"Al'ummar Falasɗinawan ƙasar Falasdin ta nan gaba"

Mista Etkes da sauran ƙungiyoyin da aka ɗora wa alhakin bibiyar ayyukan sun yi gargadin cewa, mamayar za ta bar mutane irinsu Mohammed Ayer a cikin wani yanki da aka yi wa ƙawanya.

Wani nazari da cibiyar binciken Amurka ta 'Washington Institute'ta yi na nuni da cewa "cikakkiyar mamayar" da Isra'ila ta yi ga sama da kashi 30% na yankin Gaɓar Yamma za ta shafi Falasdinawa 110,000.

Mista Netanyahu ya ce waɗanda ke zaune a gangaren Jordan, ga misali za su kasance "ƙarƙashin mulkin Falasɗinawa."

Masu sukar lamirin manufar sun yi fargabar cewa, wannan na nuni da cewa mutanen za su zauna ne a tsibiran da gwamnatin Falasdinawa ke iko, amma kewaye da kasar da ke karkashin hurumin Isra'ila.

Palestinian village of Qirah, south of Nablus, with Israeli settlement of Ariel in background (22/06/20)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ƙauyukan Falasɗinawa da matsugunan Yahudawa na kallon juna a wasu yankuna

Shugabannin Falasɗinawa, da ƙwararru kusan 50 da Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta naɗa sun ce hakan zai tabbatar da tsarin "nuna wariya" a Gaɓar Yamma - wato mutum biyu na ƙarƙashin mulkin ƙasa guda kuma a wuri guda, ba tare da daidaiton 'yanci ba.

Wasu jiga-jigan 'yan adawa daga jam'iyyu masu rinjayen Yahudawa na ganin shirin a matsayin wani abu mai matukar tayar da hankali, wanda ake aiwatarwa kara-zube.. Suna ganin nasarar yin gaban kai wajen haɗe yankunan a matsayin wata 'yar ƙanƙanuwa, yayin da kuma mutuncin Isra'ila ya zube a idon duniya.

Sai dai a ganin Birgediya-Janar Yossi Kuperwasser mai rataya adadin Falasdinawan da aikin mamayar ya ritsa da su "bai taka kara ya karya ba." Ya ce da yawansu za iya samun damar mallakar gida ta Isra'ila a mataki na wucin gadi, inda ya yi nuni da cewa kamata ya yi shugabancin Falasɗinawa ya fahimci gwamnatin Trump.

"Wannan shi ne azancin shirin zaman lafiyar Amurka," in ji shi. "Falasɗinawa za su kasance 'yan kasar Falasɗin da za a kafa nan gaba."

'Ba za mu yi watsi da aikinmu mu koma gida ba'

Tafiyar mota zuwa birnin Faladinawa na Ramallah ya cika sarƙaƙiya. Birnin na da hanyoyin shiga da fita 'yan kadan, sannan gagarumin cunkoson ababen hawa ya zama ruwan dare.

Ramallah ne babbar hedikwatar Gwamnatin al'ummar Falasɗinawa.

An kafa gwamnatin mulkin ne sanadiyyar 'yarjejeniyar Oslo a shekarun 1990, wadda ta kai matuka a kokarin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Yanzu a ƙoƙarin ƙara matsin lambar ƙasashen duniya don kauce wa mamaya, Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce Gwamnatin al'ummar Falasɗin ta daina mutunta da Isra'ila ta ƙulla da Amurka, kan batun tsaro.

Yitzhak Rabin (l), Bill Clinton (c) and Yasser Arafat at signing of the Oslo Accords in Washington (13/09/93)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A 1993 Isra'ila da Falasɗin suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya amma sun gaza cimma matsaya kan wajewar ƙarshe

Wasu na fargabar cewa jingine irin wannan aikin haɗin gwiwa, na iya haddasa rushewar Gwamnatin Falasdinawa, da janyo tsunduma cikin zaman kara-zube a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Yayin da ake cikin mummunar siyasar rarrabuwar kai a Falasɗin, ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas - babbar mai adawa da ƙungiyar Fatah ta Shugaba Abbas - na cin gajiyar halin da ake ciki, kuma tana ma gargadin yiwuwar shiga takun-saƙa da Isra'ila.

Na halarci taron manema labaran da fira ministan Falasdinawa, Mohammad Shtayyeh ya kira. A ko da yaushe dai ana tsaurara matakan tsaro ne. Yanzu kuma akwai matakan wanke jiki don yaƙi da cutar korona kafin a bari ka shiga ginin - na shiga cikin wani ɗan ɗaki inda aka kwarara mini sinadarin tsaftace jiki, wanda galibi na wanke kaina jagab da shi.

Annobar sannu a hankali kutsawa cikin ginin, amma dai ba ta tsayar da harkokin shugabancin yankin ba.

Fira minista Shtayyeh ya yi imani shirye-shiryen Isra'ila na kawo rikicin zuwa wani sabon matsayi a tarihi.

"Wannan shirin zaman lafiya ya gamu da wata gagarumar kiki-kaka," in ji shi. "Muna tunkarar wani lokaci na tsage gaskiya a matsayinmu na shugabannin Falasdinawa."

Na dai bijiro da batu game da makomar Gwamnatin Falasdinawa.

"Kada mu yaudari kanmu," ya amsa. "Shugabancin al'ummar Falasdinawa ba kyauta ba ce daga wani mutum. Ta kafu ne saboda kasancewar al'ummar Falasɗinu.. Ba za mu watsar da shi, mu koma gida, mu tsugunna ba."

Mista Shtayyeh ya zargi al'ummar duniya da gaza daukar mataki.

Me ya sa gwamnatinku ba za ta zauna da Amurka don tattaunawa ba, aka tambaye shi.

Ya ce haɗe yankunan Gaɓar Yamma daidai yake da "ruguza" makomar ƙasar Falasdinawa, kuma tunanin ma a amince da hakan zai sa gwamnatin Falasdinawa ta zama tamkar "taron maciya amana - ba kuma za mu taɓa zama haka ba."

'Tafiya a kan siratsi'

Me zai faru nan gaba? Mista Netanyahu ya ci gaba da bayani game da shirye-shiryensa, duk da cewa raɗe-raɗin cewa wata yaudara ce don samun goyon bayan masu ra'ayin rikau a zaɓuka guda uku da suka gaza kayawa.

"Waɗannan yankuna, su ne inda aka kafa ƙasar Yahudawa har ta bunkasa," fira minista ya yi game da matsugunnan 'yan kama-wuri-zaunan, lokacin da ake daf da rantsar da sabuwar gwamnatinsa ta haɗin gambiza a watan Mayu.

"(Aiki da dokokin Isra'ila a cikinsu) ba zai nisanta mu da zaman lafiya ba, zai ma kusantar da mu ne gare shi."

Benjamin Netanyahu gestures towards Israeli settlement of Har Homa (20/02/20)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haɗe yankunan zai sake shata iyakar gabashin Isra'ila