Jerry Rawlings: Tsohon shugaban ƙasar Ghana ya rasu

Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya rasu yana da shekara 73 a duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wata majiya a fadar shugaban kasar tana cewa Mr Rawlings ya mutu ne da safiyar ranar Alhamis a Accra babban birnin kasar.
Rahotanni daga kasar sun ce tsohon shugaban Ghana ya mutu ne a wani asibiti bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
A matsayinsa na babban jami'in sojin Sama na Ghana, ya jagoranci juyin mulki sau biyu, na farko da 1979, sannan ya mika mulki ga gwamnatin farar hula, amma ya sake yin juyin mulki shekara biyu bayan hakan.
Ya gudanar da mulkin soji har lokacin da aka koma kan tsarin mulkin siyasa mai jam'iyyu da dama a 1992, inda aka zabe shi a matsayin shugaban farar hula. Ya sauka daga mulki a 2001 bayan ya kammala wa'adi biyu na mulki.
Mr Rawlings mutum ne mai kwarjini, wanda ya kwace mulki a 1979 domin yaki da cin hanci.
A watanni kadan da ya yi yana jagorancin kasar a 1979, ya dauki naiyun kashe da dama daga cikin tsofaffin shugabannin kasar da Janar-Janar na rundunar soji saboda zargin cin hanci da almubazzaranci.
Ana kallonsa a matsayin mutumin da ke son talakawa wanda ya soma mulki a matsayin dan gurguzu.
Daga bisani ya kaddamar da tsarin tattalin arziki na kasuwa ta yi halinta sannan ya tabbatar da wanzumar mulkin dimokradiyya, wanda ake ci gaba da shi a yanzu, bayana kasar ta sha fama da juyin mulki a shekarun 1960 da 1970.

Asalin hoton, Getty Images











