Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa El Rufa'i ya tilasta wa kowanne baligi biyan harajin 1,000 a Kaduna
Masu sharhi da al'ummar a jihar Kadunan Najeriya sun fara bayyana ra'ayoyinsu dangane da sabon harajin naira 1000 kan kowane baligi a kowace shekara, da hukumar tattara harajin jihar za ta fara aiwatarwa a sabuwar shekara mai kamawa.
Shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da kuɗin ne wajen gina jihar.
Wannan doka ce da ta shafe shekaru a rubuce, amma aiki da ita shi ne ya zama abu mai wuya, in ji Dakta Tijjani Naniya wani masana tarihi a Najeriya.
''Ko a lokacin Turawan Mulkin Mallaka ana biyan harajin kashi-kashi, ana biyan na mutane wanda kai tsaye ake kiransa haraji, sai wanda ake kira jangali wanda ya shafi dabbobi da abubuwan amfani na yau da kullum.
''Sai dai bayan samun ƴancin kai aka dakatar da karɓar wannan haraji, abin da ya sanya mafi yawan mutanen da suke ƙasa da shekara 30 ba su san an taɓa karɓar wani abu mai kama da haraji ba a baya,'' in ji Dakta Naniya.
Dawo da wannan doka ta biyan harajin naira 1,000 da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa'i ya yi a wannan lokaci, ta haɗu da tsaiko tare da shan suka daga mutane daban-daban.
A ranar Laraba ne hukumar haraji ta jihar ta sanar da dawo da karɓar wannan haraji, wadda ta ce wajibi ne ga duk wanda ya haura shekara 18 ya riƙa biyan naira 1,000 duk shekara a matsayin haraji.
Ta ce za a rika amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen aikin ci gaban ƙasa ga al'ummar da suka biya.
Sai dai hakan ya sanya mutane da dama mayar da martani kan saƙon.
Wannan ya ce bai fahimci me yasa za a ce dole ne biyan ba? Daga ina wannan abin ya fito? Har yanzu ban ga sanarwar da ta ce dole ƴan Najeriya su biya haraji ba.
Ko Jihar Legas da matsalar zanga-zangar Endsars ta shafa wannan ba zai taɓa zama dalili ba ko da minti ɗaya.
Jihar da ba za ta iya kare mutanenta ba. Almajirai da masu bara nawa ne za su iya biyan naira 1,000. Kun san waɗanda suke hara da wannan haraji.
Matsalar Tattalin Arziki
Duk da cewa ana fama da matsalar tattalin arziki a faɗin duniya, amma gwamnatin Kaduna ta fito da wannan sabon tsari.
A gefe ɗaya wasu na kukan ba su warware daga koma bayan da annobar korona ta janyo ba, kuma an fito da wannan batu.
To amma su ma gwamnatoci suna kukan cewa su ma suna fuskantar wannan matsala.
Wasu kuma na ganin waɗanne ayyuka ake so a yi lokacin da ake fama da matsalar tsaro.
Ko an yi ayyukan raya ƙasar da gwamnati ke iƙirari, su wane ne za su amfana ganin cewa babu wata nutsuwa ga waɗanda za su amfana da ayyukan.
Al'ummar jihar Kaduna na ta kukan cewa ba wannan ne karon farko da Gwamna El-Rufa'i yake sanya dokoki masu tsauri ba gare su, ba tare da kallon masu ƙaramin ƙarfi ba daga cikin al'umma.