Hukumar FAO: Abuja da jihohin Najeriya 16 na fama da karancin abinci

    • Marubuci, Salihu Adamu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Wani rahoto da hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa mutane miliyan goma daga jahohi 16 a Najeriya na fama da 'yunwa ciki har da babban birnin tarayyar kasar Abuja.

Rashin samun ingataccen abinci matsala ce da ta dade tana ci wa kasashen nahiyar Afirka tuwo a kwarya.

Hukumar FAO ta ce duk da sassauta dokar kullen annobar korona da aka yi, har yanzu mutane da dama na shan wahala wajen samun abin da za su ci.

Rahoton hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2020 ya lissafo jihohin Adamawa da Gombe da Bauchi da Borno da Jigawa da kuma Kano a cikin wadanda al'umominsu ke fama da yunwa.

Sauran sun hada da Katsina da Kebbi da Neja da Filato da Sokoto da Taraba da Zamfara har ma da Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

Hukumar ta FAO ta ce daga yanzu zuwa watan Agustan shekarar 2021 akwai bukatar yin hanzari domin ceto al'umma kusan miliyan 14 daga fadawa tarkon yunwa a wadannan jihohi.

Girman matsalar a jihar Adamawa

A cikin wannan makalar BBC ta yi duba kan yadda iyalin wani gida ke fama da matsalar rashin isashshe kuma ingantaccen abinci a Yola fadar jihar Adamawa.

Na tafi har cikin gidan da iayalan wannan gidan da ke unguwar Wuro Dole a Yola fadar jihar Adamawa domin gani ma ido na halin da suke ciki.

Mun tashi daga makwabciyar unguwar, wato Wuro Cekke.

Tafiyar minti biyar ce kawai daga Wuro Cekke zuwa Wuro Dole amma fa sai da abin hawa. Don haka muka hau keken A Daidaita Sahu.

Wuro Dole dai unguwa ce da mutane iri biyu ne kawai ke zaune a cikin ta. Masu matsakaicin karfi da kuma 'yan rabbana ka wadata mu.

A unguwar ta Wuro Dole, na isa kofar gidan wani malami mai suna Muhammad.

Gidan Mallam Muhammad

Gida ne da aka gina da laka kuma yana dauke da dakuna biyar da zaure daya, kyauren shiga gidan na kwano ne sannan akwai bishiyoyin Mangwaro guda biyu a cikin gidan.

Ga yadda tattaunawar BBC ta kasance da Mallam Muhammad:

Mutum nawa ke cikin wannan gidan naka?

"Ina da yara goma sha daya da mata biyu da sauran su. A takaice mu goma sha bakwai ne ke zama a wannan gida."

Yaya batun samarwa mutane dake karkashinka isashshe kuma ingantaccen abinci?

"Samun isashshe kuma ingantaccen abinci a zamanin mu na yau sai dai kawai iya gwargwado amma isasshshe ko ingantacce kam da wahala."

Sana'ar me kakeyi domin dogaro da kai?

"A shekarun da suka gabata ina aiki da jami'ar Amurka da ke Yola kusan shekara 16 amma watanni bakwai da suka gabata an sallami ma'aikata kuma abin ya shafeni. Bana dai noma kawai na yi abin dogaron ke nan."

Jami'ar tayi bayani cewa akwai kudaden sallama data bawadanda abin ya shafa, shin wace sana'a ka fara da aka baka wadannan kudaden?

"Gaba dayanmu wadanda na sani aka sallama albashin wata daya ne kawai aka sallame mu da shi."

Yaya rayuwa take wajen daukar dawainiyar mutane 17 dake karkashin ka?

"Gaskiya akwai wahala kwarai domin daukar dawainiyar mutum 17 ba abin wasa ba ne. Muna jira dai muga abin da Allah zai yi."

Ana iya samun abinci sau uku a rana?

"Alhamdulillah wata rana ana samu wata rana kuma ana samu safe da yamma kadai da ikon Allah. Haka dai muke lallabawa."

Sharhi

Wannan rahoton na rashin isashshen abinci da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na bana ya nuna bukatar mayar da hankali da gaggawa kan jihohin Najeriya 16 da yawancin al'umominsu ke fama da matsalar yunwa.

Ba abin mamaki ba ne idan aka ce za a samu matsalar yunwa a shekarun 2020 zuwa 2021 a kasashen Afirka saboda manyan abubuwa uku da suka faru.

Na farko shi ne yadda annobar korona ta jefa tattalin arzikin kasashen duniya da dama cikin masassara.

Na biyu shi ne fari da damunar bana ta zo da shi inda ruwa ya dauke a yankuna da dama ba tare da amfanin gona ya gama nuna ba.

Sannan na uku shi ne yanda zugar farin dango ta lalata amfanin gona mai yawa a kasashen gabashin Afirka.